Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
Published: 27th, November 2025 GMT
Daga Isma’il Adamu
Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar.
Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace.
Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa su haura kashi 30 cikin ɗari.
Gwamna Radda, wanda ya bayyana kasafin a matsayin “kasafin jama’a,” ya ce an tsara shi ne daga shawarwarin da aka tattara a tarukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Yayin da yake jinjinawa ‘yan majalisar dokokin jihar bisa kyakkyawar alakar aiki da suke da ita da bangaren zartarwa, gwamnan ya bukaci kwamitocin majalisar su gudanar da aikinsu na sa ido don tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin yadda ya kamata.
Tun da farko, yayin mika kudirin kasafin domin rattaba hannu, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasir Yahaya, ya ce ‘yan majalisar sun duba tare da amince da kasafin cikin makonni uku, lamarin da ya sanya Katsina ta zama jihar farko da ta samu dokar kasafin kudin shekara ta 2026.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC
A yau Litinin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai yankin kati domin shiga Jam’iyyar ADC a hukumance.
Manyan hidiman Atiku sun shaida wa Aminiya cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yin rajistar Atiku a mazaɓarsa ta Jada 1 da ke Ƙaramar Hukumar Hada ta Jihar Adamawa.
Atiku ya yi nuni da wannan mataki ne a wani taro da ya gudanar da shugabannin ADC na Jihar Adamawa a Yola, inda ya ce: “A Najeriya gaba ɗaya akwai sabon motsi na siyasa, ko ba haka ba? Yau wannan motsi ya kai mu ina? ADC. Don haka, jama’ar Adamawa da Najeriya, jam’iyyarmu yanzu ita ce ADC, shugabanninmu kuma suna nan a zaune.”
Ya ƙara da cewa: “Bayan haka, a ranar Litinin zan kasance a hukumance cikin ADC. Kafin yanzu ban shiga ba; ku ne kuka riga ni. Za ku karɓe ni?”
Tun da farko ana ta shakku kan irin jajircewar Atiku da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Lam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ga ADC, bayan da ƙungiyar adawa da suke jagoranta ta amince da jam’iyyar a matsayin dandalin ta na zaben 2027.
Rashin halartar Atiku da Obi wajen ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ADC a makon da ya gabata ya ƙara haifar da tambayoyi kan ko suna nan daram da matsayar ƙungiyar.