DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
Published: 26th, November 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.
Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.
Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a akai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Haramta kudin fansa karban kudin fansa masu garkuwa Masu Garkuwa da mutane
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita.
Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita.
Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan.
A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar Sikila a duniya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan cutar amosanin jini don gano yadda masu fama da ita ke ji a rayuwar su.
Domin sauke shirin, latsa nan