Tinubu Ya Janye ‘Yan Sanda Daga Tsaron Manyan Mutane, Ya Amince Da Daukar Sabbin 30,000
Published: 24th, November 2025 GMT
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar da ayyukan ƙasa.
Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar sojin sama, da na ƙasa da na ruwa da Darakta Janar na ma’aikatar tsaro ta DSS da kuma Sufeto Janar na ƴansanda Kayode Egbetokun.
Sanarwar ta ce, daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa to ya nemi jami’an tsaron Nigeria Security and Civil Defence Corps.
Shugaban ƙasa ya ɗauki wannan mataki ne la’akari da cewa sassan Najeriya da dama, musamman a yankunan karkara ana fuskantar ƙarancin jami’ai ofisohin ƴansanda, lamarin da ke sanya wahalar sauye nauyin kare al’umma da aka ɗaura musu.
Tuni Shugaba Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin jami’an ƴan sanda 30,000, yayin da gwamnatin tarayya ta sanar da wani shirin haɗin gwiwa da jihohi don haɓaka cibiyoyin horar da ƴan sanda a duk faɗin ƙasar.
Daga BELLO WAKILI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Amincewa Daukar Sabbin Manyan Mutane Tsaro Ya Janye
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa an ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kubutar dalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja.
“Godiya ga jami’an tsaronmu a ‘yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara,” in ji shi. Sai dai ba yi karin bayani ba kan yadda aka ceto su.
“Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a kasa baki daya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan ke faruwa,” in ji shi.
“Haka nan, ina mai farin ciki cewa an gano 51 daga cikin daliban makarantar Catholic School ta jihar Neja.”
Tun da farko, kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce ɗaliban sun gudu ne daga hannun masu garkuwar tsakanin ranakun Juma’a da Asabar bayan sace su a ranar Alhamis da dare.
Wannan yana daya daga cikin manyan garkuwa da mutane a cikin ‘yan shekarun nan, a yankin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke kai hari akai-akai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba November 23, 2025 An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran November 23, 2025 An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka November 23, 2025 Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci