Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar
Published: 25th, November 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu suna iya kawo karshen yarjeniyar zaman lafiya da ta cimma da ita.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, kungiyar Hamas ta aiwatar da dukkan sharuddan tsagaita wuta wadanda aka dora mata, amma bangaren HKI ya ci gaba da keta tsagaita wutar tare da hare-haren da take kaiwa kan yankuna daban-daban na zirin Gaza, hare-haren da suka kai daruruwan Falasdinawa ga shahada ya zuwa yanzu.
Qassem ya ce tuni kungiyar ta shaidawa jami’an gwamnatin kasar Masar kan abinda HKI take yi na keta hurumin yarjeniyar tsagaita budewa juna wutan wanda bai kai watanni biyu ba.
Kasashen Masar, Turkiya da Qatar da Jordan da wasu kasashen larabawa da Musulmi suna daga cikin kasashen da suka dauki nauyin ganin an aiwatar da shirin tsagaita wutar kamar yadda ya dace. Amma tun bayan tsagaita wuta yahudawan basu daina kashe Falasdinawa ba. Banda haka sun ci gaba da takaita kayakin abincin da ke shigowa Gaza sabanin abinda aka cimma da ita.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia
Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Habasha sun rattaba hannu ne akan yarjejeniyar aikin soja a tsakaninsa a wurin baje kolin jiragen sama na wannan shekara ta 2025 a birnin Dubai.
A bangaren Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya wakilce ta shi ne Janar Ibrahim Nasir al-Alawi, wanda wakilin ma’aikatar tsaro ne, sai kuma janar Rashid Muhammad al-Shamsi da shi ne kwamandan rundunar sojan sama.
A bangaren kasar Habasha kuwa wanda ya wakilce ta kuwa shi ne kwamandan rundunar sojan Saman kasar Laftanar janar Yilma Midasa Janaba.
Kasashen biyu dai suna da alaka a fagen aikin soja, da a shekarar 2019 ne su ka fara rattaba hannu akan yarjejeniyar aikin tare a wannan fagen.
A shekarar 2023 ma dai kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar fahimta juna da aiki tare a birnin Addis Ababa. Fagagen da wannan yarjejeniyar ta kunsa sun hada tattalin arziki, kai da komowar kudade, zuba hannun jari da kuma fada da ayyukan ta’addanci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran November 23, 2025 An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka November 23, 2025 Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump November 23, 2025 Venezuela Ta Gargadi Amurka Kan Shirin Tada Hankali A Kan Iyakokin Kasar November 23, 2025 CAN: Yawan Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ranar Jumma’a Sun Fi 300 November 23, 2025 Ribadu Ya Gana da Sakataren Yakin Amurka Kan Batun Kashe Kiristoci A Nijeriya November 22, 2025 Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki November 22, 2025 Isra’ila Ta Kashe Yara Falasdinawa Guda 22 A Yankin Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci