Iran Da Omman Sun Tattauna Kan Al-Amuran Yankin Da Kuma Dangantaka Tsakaninsu
Published: 24th, November 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo al-amura da suka shafi halin da ake ciki a yankin musamman HKI da kasashen yankin, da kuma dangane da kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Ommam ta taka rawar a zo a gani a kokarin kasar Iran na kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma shiga tsakanin Iran da kasashen yamma dangane da shirin kasar na makamashin Nukliya.
Ziyarar da Aragchi ya kai Muscat dai yana daga cikin shirin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na tuntubar kasashen makobta daga lokaci zuwa lokaci saboda kara dankon zumunci da su da kuma musayar ra’ayin kan al-amuran da suke faruwa a yankin Asiya ta kudu da kuma duniya.
Ministan harkokin wajen kasar Omman Badr Al-Busaidi ya godewa Aragchi da wannan ziyarar ya kuma bayyana cewa kasarsa a shirye take ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Asia ta kudu, sannan ya yi kira da a yi amfani da hanyoyin tattaunawa don warware matsalolin da ke tasowa tsakanin kasashen yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci Daukar Matakan Da Suka Dace Kan Ta’asan Da HKI Ta Aikata A Beirut November 24, 2025 Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut November 24, 2025 Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno November 24, 2025 Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA) November 23, 2025 Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu November 23, 2025 ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar
Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka yana takurawa kasarsa ta amince da al-amura guda 28 da ya gabatar wanda a fadinsa zai kawo karshen yakin shekari kimani 3 wanda kasarsa take fafatawa da kasar Rasha.
Labarin ya kara da cewa daga cikin al-amuran da shugaban ya gabatar a wannan shirin kawo karshen yaki a Ukraine sun hada da amincewa da zaben raba gardaman da aka gudanar a shekara 2014 wanda ya hade tsibirin Cremea da kasar Rasha, amincewa da mamayar da kasar Rasha tayiwa yankin Donesk da Luganks wadanda suka zabi kasancewa bangaren kasar Rasha har’ila yau da kawo karshen burinta na zama mamba a cikin kungiyar tsaro ta NATO.
Trump ya bukaci Ukraine ta kawo karshen samuwar sojojin kasar a dai-dai wuraren da take fafatawa da kasar Rasha a halin yanzu.
Kakakin fadar kremlin Dmitry Peskov ya yi kira ga shugaba Zelesky ya amince da tattaunawa da kuma fahintar juna a kan wannan yakin, ko kuma ya fuskanci hatsarin kara rasa wasu yankuna na kasarsa.
Shugaban dai yana cikin tsaka mai wuya, saboda rashin amincewa da shawarwarin da shugaba Trump ya gabatar zai sa kasar Ukrai ta rasa babban aboki kamar Amurka. Sannan a dayan bangaren kuma amincewa da wadan nan shawarwari kaskanci ne da rashin mutunci ga kasarsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yan Wasan Kasar Iran Sun tashi Da Lambobin Yabo 81 A Wasannin Zumunci Tsakanin Kasashen Musulmi November 22, 2025 Shugaban Rasha yace Ba zai Janye Ayyukan Soji Da Yake Yi A Kasar Ukrain Ba November 21, 2025 Kwamitin Sulhu Na MDD Ya yi Tsokaci Kan Rashin Tsaro A Najeriya November 21, 2025 Araqchi: Iran Ta Shirya Tsaf Fiye Da Kowanne Lokacin Musamman Bayan Yakin Kwanaki 12 November 21, 2025 China ta ce Ya Kamata A Aiwatar Da Sakamakon Taron Kolin Tianjin Don Inganta Kungiyar SCO November 21, 2025 Iran Ta yi Gargadi Game Da Sakamakon Da Zai Iya Faruwa A Yankin Bayan Shigar Isra’ila Kasar Siriya November 21, 2025 Araqchi: Yarjejeniyar Da Aka Cimma Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA A Kasar Masar Ta Rushe November 21, 2025 Kakakin Rundunar ‘IRGC’: Yakin Kwanaki 12 Ya Nuna Karfin Kariyar Makaman Masu Linzamin Iran November 21, 2025 Iran Da Wasu Kasashe Bakwai Sun Mayar Da Martani Kan Hudurin IAEA Kan Kasar Iran November 21, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Kiran Da A Sanya Isra’ila Cikin Jerin Masu Aikata Abin Kunya Saboda Kashe Yara November 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci