Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya
Published: 23rd, November 2025 GMT
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission Substation da ke Owerri, Jihar Imo, lamarin da ya janyo fargaba da tayar da hankali ga ma’aikatan da ke wurin.
A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na ƙasa ya fitar, NUEE ta ce wannan hari na nuna take haƙƙin ma’aikaci, kuma ba za a lamunta da shi ba.
NUEE ta bayyana cewa ba za ta yi shiru ba yayin da tsaro da mutuncin mambobinta ke fuskantar barazana ba.
Sanarwar ta ce, “Wannan hari da jami’an tsaro suka kai ya saɓa wa duk ka’idojin aikin yi. Jami’anmu na gudanar da aikinsu ne na yau da kullum, amma aka afka musu da duka da barazana. Mun gaji da irin wannan cin zarafi.”
Ƙungiyar ta gargaɗi gwamnati da shugabannin rundunar ’yan sanda da cewa za ta rufe dukkan tashoshin wutar lantarki a sassan ƙasar, muddin ba a ɗauki matakin hukunta masu laifin da kuma bada tabbacin tsaron ma’aikata ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Lantarki Yajin aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Hadin Gwiwa na Faɗaɗa Bincike Don Ceto Daliban da Aka Sace a Neja
Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.
Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba.
Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban.
Ya kuma ce daga bisani za a ɗauki mataki kan hukumomin makarantar saboda ci gaba da karatu bayan umurnin kulle makarantu a yankin saboda barazanar tsaro.