Aminiya:
2025-11-23@07:03:05 GMT

An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi

Published: 23rd, November 2025 GMT

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi.

A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare, tare da bayyana cewa ba da jimawa ba za a kuɓutar da ɗaliban cikin nasara, idan komai ya tafi yadda ake so.

An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF

Ya nemi goyon bayan al’umma, yana mai cewa, “Haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci domin ganin an kammala wannan aiki lafiya lau, tare da dawo da yaran cikin iyayensu ba tare da wata matsala ba.”

A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan bindiga suka kai mummunan hari makarantar ta Maga, inda suka yi awon gaba da ɗalibai mata 25, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma musamman ma iyayen yaran.

Ministan ya ce tun bayan faruwar lamarin, Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin jami’an tsaro, ciki har da rundunar sojin sama da ta ƙasa, waɗanda ke aiki tare domin gano hanyar shiga ba tare da hallaka ko jikkata ɗaliban ba.

Ya ce, “Mun gano wurin da aka tsare yaran kuma da Yardar Allah za mu ceto su nan ba da jimawa ba. A yanzu haka muna a matakin ɗaukar tsattsauran mataki cikin hikima, domin tabbatar da cewa babu wata illa da za ta same su.”

“Ina kira ga al’ummar Kebbi da su ci gaba da haƙuri da kuma bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro. A irin wannan lamari, bayanan sirri daga jama’a na da matuƙar muhimmanci,” in ji shi.

Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi

A bayan nan ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaron da ya koma Jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗaliban da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar.

Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda ya bayyana umarnin a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis, ana sa ran Matawalle zai isa Birnin Kebbi da safiyar Juma’a.

“Yana da ƙwarewa sosai wajen fuskantar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023,” in ji sanarwar.

“A ranar 26 ga watan Fabrairu, 2021, ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 da 17 a makarantar kwana ta GGSSS Jangebe, Jihar Zamfara. ’Yan bindigar sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwar da su a ranar 2 ga watan Maris, 2021.”

Aminiya ta ruwaito cewa, shi ma dai Shugaba Tinubu ya ɗage tafiyarsa da aka tsara zuwa Johannesburg, Afirka ta Kudu, da Luanda a ƙasar Angola, domin ci gaba da samun rahotannin tsaro kan satar ɗaliban na Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a cocin Eruku da ke Jihar Kwara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan bindiga da ɗalibai

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya.

Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya.

Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja

A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro.

Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da kuma kauce wa duk wata barazana.

Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da waɗanda ke Zariya, Daura, Sakkwato, Potiskum, Ikare-Akoko, Abaji, da sauransu.

Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ake kai wa makarantu ke ƙara tsananta.

A Jihar Kebbi, ’yan bindiga sun kai hari makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School da ke Maga, inda suka sace ɗalibai 25, tare da kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makaku, yayin da yake ƙoƙarin kare su.

Rahotanni sun nuna cewa daga 2014 zuwa 2022, an sace yara sama 1,680 a makarantun Najeriya.

Gwamnati ta ce rufe makarantun na wucin gadi ne, domin kare ɗalibai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba
  • Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya
  • Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya
  • Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 
  • ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Rundunar Hadin Gwiwa na Faɗaɗa Bincike Don Ceto Daliban da Aka Sace a Neja
  • ’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 25 a Jihar Kebbi