Aminiya:
2025-11-23@19:16:10 GMT

An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu

Published: 23rd, November 2025 GMT

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara.

’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka da Kogi a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.

ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji

A cikin wani sako da Tinubu ya wallafa a X a ranar Lahadi, ya ce yana bibiyar yanayin tsaro a fadin kasar nan, kuma zai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kare ’yan Najeriya.

An yada bidiyon yadda maharan suka shiga cocin suka yi awon gaba da masu ibada yayin da suke tsaka da addu’a.

Lokacin da maharan suka dinga harbe-harbe a ciki cocin, wani Fasto ya jagoranci jama’a inda suka nemi mafaka.

Ya kuma ce an ceto dalibai 51 da aka sace a Jihar Neja.

Tinubu ya kara da cewa: “’Yan uwana ’yan Najeriya, za ku iya tuna cewa na soke zuwa taron G20 da aka yi a Afirka ta Kudu domin na mayar da hankali kan sha’anin tsaro a gida.

“Ina yi wa jami’an tsaro godiya kan aiki tukuru da suka cikin kwanaki biyun da suka wuce, an ceto dukkanin masu ibada 38 da aka sace a Eruku, a Jihar Kwara.

“Ina kuma farin ciki cewa an gano dalibai 51 daga cikin wadanda aka sace a wata makaranta a Jihar Neja.

“Ina bibiyar sha’anin tsaro sosai kuma ina samun rahotanni kai-tsaye. Ba zan yi kasa a gwiwa ba. Kowane dan Najeriya yana da ’yancin samun tsaro, kuma a karkashin jagorancina, za mu kare wannan kasa da mutanen ciki.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan bindga Kwara Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Umaurci Matawalle Ya Koma Kebbi a Cigaba da Kokarin Kubutar da Daliban da Aka Sace

Daga Bello Wakili

Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar.

An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace.

’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin  ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin.

Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Idan za a iya tunawa ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, ’yan bindiga sun sace ɗalibai mata 279 da ke tsakanin shekaru 10 zuwa 17 a Makarantar Sakandare ta Kimiyya ta ’Yan Mata da ke Jangebe, a Jihar Zamfara. ’Yan bindigar sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwa da su a ranar 2 ga Maris 2021.

Shugaba Tinubu ya ɗage tafiyarsa da aka shirya zuwa Johannesburg, Afrika ta Kudu, da kuma Luanda, na kasar Angola, domin ya jira bahasin halin da ake ciki game da ’yan matan makarantar da aka sace a Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada na Cocin Christ Apostolic da ke Eruku, Jihar Kwara.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu
  • An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi
  • ’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
  • ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Rundunar Hadin Gwiwa na Faɗaɗa Bincike Don Ceto Daliban da Aka Sace a Neja
  • ’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
  • Tinubu Ya Umaurci Matawalle Ya Koma Kebbi a Cigaba da Kokarin Kubutar da Daliban da Aka Sace