Aminiya:
2025-11-25@22:19:41 GMT

An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia

Published: 26th, November 2025 GMT

Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies.

Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci.

An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba

Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci gaba ɗaya.

Indonesia na daga cikin ƙasashen da har yanzu ake cin naman karnuka da kyanwa, duk da cewa wasu birane sun daina wannan al’ada a ’yan shekarun nan.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun yaba da sabon matakin, suna mai cewa ya dace da manufofin kare lafiyar al’umma.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane da dama kan mutu da cutar rabies a kowace shekara a Indonesia, inda rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa mutane 25 suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris 2025.

Duk da cewa a yawancin yankunan Indonesia ana kallon karnuka a matsayin dabbobin da ba su da tsabta, wasu ƙananan ƙabilu na ci har yanzu, musamman ma saboda samun naman a farashi mai sauƙi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jakarta Kare Karnuka Kyanwa

এছাড়াও পড়ুন:

Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta

Ƙungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara kanana a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da sace-sacen mutane da ake kai wa wasu makarantu a arewacin kasar.

Amnesty ta ce ta na nuna damuwa akan yadda gwamnatin Najeriya ke kara nuna gazawa a wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu musamman ma yara ‘yan makaranta.

Isa Sanusi, shi ne daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa, abin da ke faruwa yanzu ya nuna cewa ilimi zai kara samun koma fiye da baya, sai dai bisa ga yadda abubuwa ke faruwa a yanzu na rashin tsaro da satar dalibai abin zai kara yin kamari.

Ya ce,” Rufe-rufen makarantu da ake yi yanzu a arewacin Najeriya, wasu yaran har abada ba za su koma makaranta ba, don haka mu muna gani wannan babban bala’i ne don haka ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ta yi abin da ya dace.”

Isa Sanusi, ya ce,”Aikin gwamnati ba wai shi ne gina kwalta gina gadar sama bane, kare dukiya da rayukan mutane shi ne abin da ya rataya a wuyan gwamnati kuma ta gaza akansa.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah November 24, 2025  Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Kwamandan Jihadi Haisam al-Tabtabai November 24, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 162 November 24, 2025 Shugaban Kasa Ya Sami Halattar Makokin Shahadar Zahra (a) A Husainiyar Imam Khomani(q) November 24, 2025 Iran Da Omman Sun Tattauna Kan Al-Amuran Yankin Da Kuma Dangantaka Tsakaninsu November 24, 2025 Iran Ta Bukaci Daukar Matakan Da Suka Dace Kan Ta’asan Da HKI Ta Aikata A Beirut November 24, 2025 Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi
  • Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta
  • Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere
  • Umarnin janye ’yan sanda daga faɗin manyan mutane na iya zama magana kawai —Shehu Sani
  • ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno
  • Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji
  • An  Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil
  • Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF