Umarnin janye ’yan sanda masu gadin manyan mutane na iya zama zance kawai —Shehu Sani
Published: 24th, November 2025 GMT
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki.
A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya.
A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane.
A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali.
Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwanaUmarnin ya kuma bayyana cewa duk wani babban mutum da ke buƙatar tsaro zai nemi jami’an hukumar tsaron fararen kaya (NSCDC).
Sai dai a martaninsa a shafinsa na X, Sanata Sani ya nuna damuwa cewa wannan umarni na iya zama magana kawai ba tare da cikakken aiwatarwa ba.
Ya rubuta cewa: “Janye ’Yan Sanda daga manyan mutane ra’ayi ne mai kyau da kuma kyakkyawan tsari duba da gaggawar buƙatun tsaron ƙasa, amma zai iya farawa kuma ya ƙare a matsayin magana kawai.”
Najeriya ta sake fuskantar tashin hankali, ciki har da hare-haren Boko Haram a Borno da kuma farmakin ’yan bindiga a jihohin Kebbi, Neja, Kwara da Borno da Bauchi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda manyan mutane Tsaro manyan mutane
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro
Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan.
A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.
H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jiharWannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi.
PSUBEB ta sanar da cewa rufe makarantun mataki ne na wucin-gadi domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar lafiya da tsaron ɗalibai da muhimmanci.
Hukumar ta buƙaci Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi, shugabannin makarantu da shugabannin al’umma da su ba da cikakken haɗin kai wajen aiwatar da umarnin, tare da zama masu kula da duk wata alama ta rashin tsaro a yankunansu.