EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi
Published: 25th, November 2025 GMT
Taron koli karo na 7 na tarrayar Turai da tarayyar Afrika, wanda aka bude a Luanda, na maida hankali kan batun diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi a karon farko.
A cewar ajandar taron, daya daga cikin manyan jigogi zai mayar da hankali kan diyya ta kudi da siyasa da ta shafi zaluncin mulkin mallaka da cinikin bayi, gami da lalacewar tattalin arziki, da al’adu da aka tara tsawon shekaru da dama.
Wannan lokaci ne da ba a taba ganin irinsa ba a wannan matakin siyasa: ba a taba sanya irin wannan batu a cikin ajandar taron da ya hada shugabannin kasashen Turai da Afirka ba.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta ware shekarar 2025 a matsayin shekarar “Adalci ga ‘Yan Afirka da kuma Mutanen da suka fito daga zuriyar Afirka ta hanyar diyya.
A cewar AllAfrica, kawai shigar da batun a cikin ajandar ya zama babban ci gaba, domin manyan biranen Turai sun dade suna guje wa batun.
Baya ga batun diyya, taron kolin ya yi magana kan batutuwa daban-daban: ci gaba mai dorewa, zuba jari, gyare-gyare ga tsarin kuɗi na duniya, rage raunin bashi, kirkire-kirkire, tsaro, da yanayi.
Kusan shugabanni 80 ne ke halartar taron, wanda João Lourenço, Shugaban Angola kuma Shugaban Tarayyar Afirka na yanzu, da António Costa, Shugaban Majalisar Turai, tare da Ursula von der Leyen suke jagoranta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar
Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu suna iya kawo karshen yarjeniyar zaman lafiya da ta cimma da ita.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, kungiyar Hamas ta aiwatar da dukkan sharuddan tsagaita wuta wadanda aka dora mata, amma bangaren HKI ya ci gaba da keta tsagaita wutar tare da hare-haren da take kaiwa kan yankuna daban-daban na zirin Gaza, hare-haren da suka kai daruruwan Falasdinawa ga shahada ya zuwa yanzu.
Qassem ya ce tuni kungiyar ta shaidawa jami’an gwamnatin kasar Masar kan abinda HKI take yi na keta hurumin yarjeniyar tsagaita budewa juna wutan wanda bai kai watanni biyu ba.
Kasashen Masar, Turkiya da Qatar da Jordan da wasu kasashen larabawa da Musulmi suna daga cikin kasashen da suka dauki nauyin ganin an aiwatar da shirin tsagaita wutar kamar yadda ya dace. Amma tun bayan tsagaita wuta yahudawan basu daina kashe Falasdinawa ba. Banda haka sun ci gaba da takaita kayakin abincin da ke shigowa Gaza sabanin abinda aka cimma da ita.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci