Aminiya:
2025-11-25@11:32:30 GMT

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa

Published: 25th, November 2025 GMT

Gwamnonin jihohin  Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya.

“Manufar taron ita ce samar da matsaya ɗaya wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke damun yankin, tare da tsara hanyar magance su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, za a yanke muhimman shawarwari a taron domin tabbatar da tsaron yankin.

’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina

Ahemba ya bayyana cewa, sakamakon ƙalubalen tsaro da wasu jihohin Arewa ke fuskanta, gwamnatin Nasarawa ta ɗauki matakan gaggawa ta hanyar shirya taron tsaro na musamman, inda za a yanke shawarar da za ta kare jihar daga duk wata barazanar tsaro.

“Ya zama wajibi ga ’yan ƙasa su taka rawa wajen magance barazanar tsaro a ƙasarmu da jihohinmu. Don haka, dole ne jama’a su riƙa ba wa hukumomin tsaro bayanai kan mutanen da ke da halin aikata laifi,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa matsalar tsaro Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwana

Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun sakandaren kwana a matsayin wani mataki na kariya ga ɗaliban makarantun.

A cikin wata sanarwa da Mamman Mohammed, kakakin gwamnan, ya ce, wannan shawara ta biyo bayan taron tsaro tsakanin Gwamna Mai Mala Buni da shugabannin tsaro a jihar, inda suka yi nazari kan abubuwan da suka faru na tsaro a makarantu a wasu sassan ƙasar nan.

Sanarwar da Babban Sakatare na ma’aikatar Ilimi na Jihar, Dakta Bukar, ya sanya wa hannu, ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana nan take har sai an samu ci gaba a lamarin.

Gwamna Buni ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi wa shugabanni, jami’an tsaro, addu’ar ci-gaba da samun zaman lafiya da ingantaccen tsaro a Jihar da ma ƙasar baki ɗaya.

An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi na saboda matsalar tsaro NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki

Daga sai gwamnan ya yi fatan alheri ga ɗaurewar harkokin tsaron Jihar tare da bayar da tabbacin ci gaba da kula da harkokin tsaro da rayukan al’ummar jihar ta kowace fuska kuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro
  • Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwana
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi na saboda matsalar tsaro
  • ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno
  • An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro
  • H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa
  • Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu
  • Gwamnatin Neja Ta Rufe Makarantu Saboda Matsalar Tsaro