Aminiya:
2025-11-24@09:06:27 GMT

Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwana

Published: 24th, November 2025 GMT

Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun sakandaren kwana a matsayin wani mataki na kariya ga ɗaliban makarantun.

A cikin wata sanarwa da Mamman Mohammed, kakakin gwamnan, ya ce, wannan shawara ta biyo bayan taron tsaro tsakanin Gwamna Mai Mala Buni da shugabannin tsaro a jihar, inda suka yi nazari kan abubuwan da suka faru na tsaro a makarantu a wasu sassan ƙasar nan.

Sanarwar da Babban Sakatare na ma’aikatar Ilimi na Jihar, Dakta Bukar, ya sanya wa hannu, ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana nan take har sai an samu ci gaba a lamarin.

Gwamna Buni ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi wa shugabanni, jami’an tsaro, addu’ar ci-gaba da samun zaman lafiya da ingantaccen tsaro a Jihar da ma ƙasar baki ɗaya.

An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi na saboda matsalar tsaro NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki

Daga sai gwamnan ya yi fatan alheri ga ɗaurewar harkokin tsaron Jihar tare da bayar da tabbacin ci gaba da kula da harkokin tsaro da rayukan al’ummar jihar ta kowace fuska kuwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Makaranta Makarantunn kwana

এছাড়াও পড়ুন:

An rufe duk makarantu a Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun sakandire na gwamnati da na masu zaman kansu nan take.

Haka kuma, gwamnatin ta rufe dukkan manyan makarantun gaba da sakandire a faɗin jihar, banda Kwalejin Nazarin Aikin Jinya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi.

An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya 

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, tare da Kwamishiyar Ilimin Firamare da Sakandare, Dokta Halima Bande, suka fitar a Birnin Kebbi, ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon barazanar hare-haren da ake samu a wasu sassan jihar a kwanakin nan.

Manyan makarantu da abin ya shafa sun haɗa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Dakingari, Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kebbi (KSUSTA) da ke Aliero, Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jega, da kuma Kwalejin Ilimi ta Argungu.

Sanarwar ta ce Kwalejin Nazarin Aikin Jinya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi ba ta cikin jerin makarantun da aka rufe.

Gwamnati ta buƙaci hukumomin dukkan makarantun da su yi wa wannan umarni biyayya, tare da kwantar da hankalin al’umma, tana mai bayyana cewa nan gaba kaɗan za a ayyana ranar komawa makarantun da zarar komai ya daidaita.

Aminiya ta ruwaito yadda a bayan nan jihohi da dama musamman a Arewacin suka bayar da umarnin rufe makarantu saboda fargabar matsalar tsaro da ake ci gaba da samu a kwanakin nan.

Wasu daga cikin jihohin da suka rufe makarantu sun haɗa da Kwara, Neja, Katsina, Taraba, Yobe da kuma Filato.

Wannan dai na zuwa ne bayan ’yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a wata Makarantar Sakandire ta Maga da ke Jihar Kebbi.

Sai kuma harin da aka samu a wani coci da ke Jihar Kwara da kuma sace fiye da ɗalibai 300 da ’yan ta’adda suka yi a wata makarantar St Mary da ke Jihar Neja.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi na saboda matsalar tsaro
  • Gwamnatin Kebbi Ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantu a Jihar
  • An rufe duk makarantu a Kebbi
  • Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar
  • Gwamnatin Neja Ta Rufe Makarantu Saboda Matsalar Tsaro
  • Gwamnatin Katsina Ta Umurci a Gaggauta Rufe Dukkan Makarantun Jihar
  • Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba
  • Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ba da Umarnin Rufe Makarantu 41 Nan Take
  • Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya