Aminiya:
2025-11-27@10:33:58 GMT

Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Published: 27th, November 2025 GMT

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma.

Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban.

’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa

A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin.

Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102.

Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin Musulunci, mai imani, tawali’u da hikima.

A cewarsa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci, koyar da Alƙur’ani, da kuma taimaka wa mutane wajen tarbiyya.

Marigayin, ya koyar da dubban ɗalibai da suka haddace Alƙur’ani tare da yaɗa addinin Musulunci a sassan nahiyar Afrika.

Gwamnan, ya ƙara da cewa gudunmawar da marigayin ya bayar a fannin tafsiri, fiqhu da tarihi sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗora al’umma kan turbar tsira.

Har ila yau, ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da girmama marigayin ta hanyar tallafa wa makarantu da manufofin da ya gina, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci, tarbiyya da ci gaban al’umma.

Ya yi addu’a rAllah ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi aAljannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa, mabiyansa da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin rashinsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Bala rasuwa ta aziyya

এছাড়াও পড়ুন:

Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba.

Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan.

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Ya ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa iyayen yara da al’ummar Kebbi cewa ’ya’yansu sun dawo lafiya.

“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro, musamman sojoji, ’yan sanda, da Civil Defence da suka yi aiki tukuru har aka kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya,” in ji Gwamnan.

Idris ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi ba ta biya kuɗin fansa ba, “Mu, a matsayin gwamnati, ba mu ba da ko sisi ba. A binciken da muka yi, babu wanda ya biya kuɗin fansar yaran.”

A ranar Litinin din da ta gabata ce ’yqn bindiga suka sace ɗaliban su 25 daga makarantar bayan sun kashe mataimakin shugaban makarantar.

Sai dai daga bisani ɗaya daga cikin ɗaliban ta gudo ’yan kwanaki bayan sace su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah
  • Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro