2025-11-23@07:01:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 443
«da ɗalibai»:
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi. A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare, tare da bayyana cewa ba da jimawa ba za a kuɓutar da ɗaliban cikin nasara, idan komai ya tafi yadda ake so. An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF Ya nemi goyon bayan al’umma, yana mai cewa, “Haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci domin ganin an kammala wannan aiki lafiya lau,...
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan. Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Asabar. Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Ya bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar. Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno A ranar Alhamis ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifukan ta’addanci. Sai dai Obi ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kuskure tun daga farko wajen tafiyar da lamarin, kuma bai kamata ya kai wannan mataki ba. Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da dama ciki har da...
Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja. Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro. Gwamnan Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar. Sanarwar da kwamishinar ilimi ta jihar, Augustina Godwin, ya fitar ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari. Don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta....
Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba. A baya Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai...
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro. Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya. Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Maharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic. Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba. Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya...
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba. Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba. Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan...
’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an yi awon gaba da ɗalibai da dama yayin harin da aka kai makarantar. ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Wata majiya daga ɗaya daga cikin coci-cocin Katolika a jihar ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa har yanzu makarantar na...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru. Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba. Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban. Ya kuma ce...
Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU. IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Aminiyar ta ruwaito cewa, ɗaliban sun yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai da shugabannin ƙungiyar a jami’o’in Bayero da kuma North West —Mudassir Adamu Musa da Asahabulkhair Labaran Usman —suka jagoranta. Ɗaliban sun bayyana cewa yajin aikin da ƙungiyar ASUU...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba a amfani da hukuncin kisa, a maimakon haka ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO) cewa ba zai kare kambunsa a kan Wardley ba. Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal WBO ta tabbatar da cewa Usyk “ya zaɓi ya ajiye kambun ne saboda wasu dalilai da suka gamsar da hukumar.” A halin yanzu, Usyk na ci gaba da riƙe kambuna uku: WBA, WBC da IBF,...
Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.
Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya. Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco. Za...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa. Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012. Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan...
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar. Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin hankali, yana mai cewa ci gaba da kai hare-hare kan makarantun Arewa barazana ce ga zaman lafiya da makomar ilimi a yankin. Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba A madadin sauran gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Kebbi, iyalan waɗanda aka sace da kuma waɗanda...
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru. “Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar. Malam Muhammad wanda idanunsa ke cike da ƙwalla ya ce, “Roƙona Allah Ya sa a dawo min da ita lafiya, ita kaɗai gare ni. Ina roƙon Gwamna Idris ya taimaka a dawo mana da su. Mun san ƙoƙarin da yake yi a fannin tsaro a tsawon shekara biyu da ya yi a kan mulki.” Shi ma Malam Aliyu Yakubu, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace,...
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga. CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano...
An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano. Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano, lamarin da ya nuna cewa ba a yi wata sanarwa ta musamman ba kafin bikin. Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC Mai taimaka wa sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da auren a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan...
Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu. Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata. Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Nsukka ta ce Gwamnatin Tarayya na lalata makomar ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar 2009. A taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi. Ya yi magana ne a madadin jami’o’i takwas da ke yankin. Opata, ya ce an tattauna tare da ƙumla yarjejeniyoyi da dama tsakanin ASUU da gwamnati tsawon shekaru, amma babu wani ci gaba da aka samu. Ya zargi jami’an gwamnati da yin lƙawarin ƙarya da gangan. Ya ce ASUU ta dakatar da yajin gargaɗin da ta yi kwanan nan saboda ɗalibai, iyaye, da ƙungiyoyin ƙwadago,...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu. Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi. Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu. Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi. Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu. Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi. Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce...
A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na yini guda kan muhimmancin rijistar haihuwa ga sabbin jarirai a duk faɗin Yankin Gwarzo na Jihar Kano. Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen gwamnati da UNICEF ke tallafawa, domin ƙarfafa tsarin kare yara da kuma tabbatar da samun damar yin amfani da muhimman aikace-aikacen zamantakewa, musamman a yankunan karkara na jihar. Wakilin NPC, Malam Abubakar Lawal, ya jaddada muhimmancin haddin kan al’umma wajen cimma nasarar...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko biyu masu zuwa. Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro “Eh, tabbas wannan shi ne Kofin Duniya na ƙarshe da zan halarta. Zan kai shekara 41, kuma ina ganin wannan ne lokacin da ya dace na ajiye takalmi,” in ji shi a wata tattanawa...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia. An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan...
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.” Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John Heitinga De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma. Roma...
Majalisar Tarayya ta amince da hukuncin cin sarƙa ga duk wani malami da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a makarantu a faɗin ƙasar nan. Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar da Dokar Hana Lalata da Dalibai ta 2025 (HB.1597), bayan tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai a ranar Laraba. Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos A ƙunshin bayanan da dokar, za a iya yanke wa duk wanda ya saɓa mata hukuncin ɗaurin shekara 14 ko shekara biyar mafi ƙaranci ba tare da zaɓin biyan tara ba. Laifukan da dokar ta bayyana a matsayin cin zarafi sun haɗa da...
Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi. Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana...
Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
Tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Najeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi abin damuwa ne da ke da ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar. Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa na X. Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Obi ya bayyana cewa, barazanar turo sojojin Amurka su yaƙi ta’addanci da ma sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurkan take da damuwa da su, lamari ne da dole dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar ya ja masa hankali. “Babu shakka...
Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi. An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Shugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na aikin al’umma da gidan rediyon ke yi, kuma suna da burin faɗaɗa shi zuwa dukkanin ƙananan hukumomin jihar 44. Ya ce, “Mu gidan rediyon al’umma ne da...
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi. NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar. A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya. Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa. “Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne...
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai October 31, 2025 Manyan Labarai Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP October 31, 2025 Manyan Labarai Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta October 31, 2025
Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira. Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta ƙara aure, wadda mahaifinsa ya ƙi goyon baya saboda abin da ya kira halin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasa. Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum A cewar lauyan masu ƙara, Barrista Lamido Abba Sorondinki, wanda ake tuhuma ya shaida...
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan. Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take fatan samu gurbin zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League ta baɗi. Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum Spalletti, shi ne kociyan da ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A a 2023, wadda ita ce karon farko cikin shekaru 33, inda...
Wani haziƙin matashin ɗan wasan Cricket mai shekara 17 ɗan asalin ƙasar Australiya ya mutu a yau Alhamis bayan ƙwallo ta buge shi a lokacin wasa. Ƙwallon ta bugi, Ben Austin a wuyansa ne duk da cewa yana sanye da hular kariyar kai (Helmet) a lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙwallon da aka bugo. Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Nan take aka garzaya da shi asibiti cikin mawuyacin hali, daga bisani rai ya yi halinsa. “Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar haziƙi Ben ɗinmu, wanda ya mutu da safiyar yau Alhamis,” in ji mahaifinsa Jace Austin a cikin wata sanarwa. A cewar jaridar ABC News, matashin...
Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye wani mai suna Stephen Adamu mai shekara 34 bisa laifin kashe ɗan uwansa. An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye a ranar 31 ga watan Junairu, 2025, kan tuhumar kashe wani David Adamu, a sashi na 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti 2021. Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Domin tabbatar da ƙarar sa, mai gabatar da ƙara Funmi Bello, ya kira shaidu shida da waɗanda ake ƙara da su gabatar da jawabi, da fom ɗin shaida da kuma wuƙa a matsayin nunin...
“Muna kira ga hukumar da sauran hukumomi su tabbatar da adalci da daidaito a lokacin ɗaukar ma’aikata na gwamnatin tarayya,” in ji shi. Shugaban Majalisar ya yaba wa Dala bisa kishin ƙasa da ya nuna, sannan ya umarci kwamitin majalisar da ya binciki lamarin tare da gabatar da rahoto domin ɗaukar mataki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU October 29, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun ci gaban al’adu da dabi’a a cikin al’umma a zahirance, da kara inganta jin dadin rayuwa, da samun manyan sabbin ci gaba wajen zurfafa shirin samar da kyakkyawar kasar Sin, da kuma kara samun ci gaba wajen karfafa garkuwar tsaron kasa. A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 (2021-2025), an kiyasta cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai zarce yuan...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin. An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru Bayanai sun ce mutuwar ɗan sa-kan ce ta jawo zargin cewa Fulani ne suka yi kisan, lamarin da ya sa wasu matasa suka dunguma suka kai farmaki a sansanin Fulani, inda suka kashe mutum goma a yayin harin. Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya ce, “kuskuren fahimta ce ta sa aka kai harin. “Sun...
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan, a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a. Ƙungiya ta tallafa wa ɗaliban makarantar masu buƙata ta musamman a Gombe ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa A yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, ya shawarci sabon Sarkin da ya ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar. A nasa jawabin, sabon Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed, ya...
Ƙungiyar Arewa Unity Women in Media, ta kai tallafi Makarantar Masu Buƙata ta Musamman da ke Gombe, domin taimaka wa gwamnati wajen kula da rayuwar ɗaliban da ke da buƙata ta musamman. Tallafin ya ƙunshi gidajen sauro, bargo da tabarmi, wanda aka raba wa ɗaliban a lokacin bikin miƙa kayan tallafin. ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Shugabar ƙungiyar, Lois Hassan daga GMTV Gombe, tallafin na da nuna kulawa da ƙauna ga ɗaliban, tare da tabbatar musu cewa al’umma ba ta manta da su ba. Ta ƙara da cewa ƙungiyar Arewa Unity Women in Media ƙungiya ce mai zaman kanta da ke gudanar da...
Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi ɗan shekara 29, mai suna Abubakar Isah Mokwa ɗalibi da yake karatun digiri na biyu a tsangayar Tattalin Arziki na Noma a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja. An kama ɗalibin ne bisa zarginsa da sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago. Rahotanni sun ce an an kama Abubakar Mokwa ne a wajen harabar jami’ar da yake da masauki a Lapai a ranar Alhamis bayan wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya caccaki gwamnan kan rashin aikin yi. ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu...
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce da fushin jama’a a faɗin jihar, inda al’umma da masu fafutuka ke kira da a bincika tare da ɗaukan mataki cikin gaggawa don hana faruwar irin haka nan gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU October 20, 2025 Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Labarai Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro October 20, 2025
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Danbare a Jihar Kano, ta gurfanar da wani mutum mai suna Malam Shaddadu bisa zargin sayar da gidan ɗansa ba tare da izini ba. Ɗan mutumin wanda ya gabatar da ƙara, Muhammad Shaddadu, ya shaida wa kotu cewa, lamarin ya samo asalin ne tun bayan da mahaifinsa ya saya wa wasu ‘yan uwansa biyu da suke uba ɗaya babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidata Sahu. APC ta rage wa Mata kuɗin tsayawa takara a Borno Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni Sai dai daga baya, tsautsayi ya rutsa da ɗaya daga cikinsu wanda ɓata-gari suka kai masa hari har suka kashe shi, kuma suka yi awon...
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi nasara a shekarar 2009. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Kano Pillars ta dakatar da Kocinta A yammacin jiya Lahadi ce aka gudanar da wasan ƙarshe a filin wasa na Estadio Nacional Julio Martínez Prádanos da ke birnin Santiago na Chile, gidan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Universidad de Chile da kuma babbar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar. ‘Yan wasan tawagar ƙwallon...
’Yan sandan da aka tura domin daƙile zanga-zangar neman a sako Nnamdi Kanu sun kama ɗan’uwansa da lauyansa, Aloy Ejimakor, inji jagoran zanga-zangar, Omoyele Sowore. A wani saƙo da ya sanya a shafin X, Sowore ya zargi ’yan sanda da kama Kanu’s ɗan uwan Kanu, lauyansa, da wasu masu ’yan ba-ruwanmu ba tare da la’akari ba. “Tawagar @PoliceNG da aka tura domin zaluntar masu zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow ta kama ɗan’uwan Nnamdi Kanu, da lauyansa @AloyEjimakor, har ma da wasu masu bin hanya. An doke sannan aka kai su ofishin ’yan sanda na Abuja. Dole ne a saki su nan take!” in ji shi. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan sanda sun yi amfani da harsashi mai rai domin tarwatsa masu zanga-zangar da ke neman...
Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Najeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zargin sa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki. Majiyoyin Aminiya sun bayyana cewa akwai zargi mai karfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoban nan da muke ciki. A ƙarshen mako ne kafofin watsa labarai na Shahara Reporters da Premium Times suka ruwaito cewa wasu hafsoshin soji 16, —waɗanda Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sun shiga hannu saboda aikata abubuwan da saɓa ƙa’idar...
Wani ɗan fashi da makami ya kai hari wani gidan biredi da ke cikin garin Kafanchan, a Jihar Kaduna, inda ya harbi ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan sannan ya yi yunƙurin tserewa da kuɗi masu yawa. Manajan gidan burodin, Abdullahi Babiyo, ya bayyana cewa suna cikin aiki lokacin da ɗan fashin, ya shiga gidan da bindiga, inda ya yi barazanar harbi idan bai buɗe masa ƙofa ba. An saki Ɗan Uwa Rano bayan tsare shi kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku Ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan da aka harba, Muhammad Abdulmumin, wanda yanzu haka yake jinya a asibiti, ya ce ɗan fashin ya shiga gidan fuskarsa a rufe da bindiga AK-47....
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda suka bayyana tsarewar tasa a matsayin mataki na keta haƙƙin ɗan Adam da kuma yunƙurin danne ƴancin ƴan jaridu. Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya Ƙungiyoyin sun buƙaci a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba, suna mai cewa tsarewar ta saɓawa...
’Yan Sanda sun saki ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano, bayan tsare shi da suka yi kan zargin ɓata sunan hadimin Gwamnan Jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo. An tsare Rano a Shiyyar ’Yan Sanda ta Ɗaya da ke Kano, bisa zargin ɓatanci. Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana tsare shi a matsayin saɓa doka da kuma ƙoƙarin danne ’yancin ’yan jarida.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin babban abokin gabar ɗan Adam. Ya ce ƙaruwar talauci a Najeriya na ci gaba da jawo rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro, da rashin fata a tsakanin jama’a. ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook domin bikin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya, Atiku, ya ce wannan rana tana tunatar da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen yaƙar talauci “Talauci ne babban abokin gabar ɗan Adam. Yana haifar da matsaloli kamar rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro da sauransu,” in...
’Yan sanda sun kama ɗan jarida Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, kan zargin ɓata sunan Babban Hadimin Gwamnan Kano kan Al’amuran Fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga Hedikwata ta Ɗaya ne suka kama Dan’uwa Rano a ranar Asabar yayin da yake aiki a ofishinsa da ke Kano. Magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan ƙara aure a Kano Gwamnati ta ɗauki matakin rage shan gishiri a Nijeriya Shaidu sun ce an kama shi ba tare da gabatar da takardar izinin kama shi ba. Ana tsare da ɗan jaridar ne bisa zargin ɓata sunan hadimin cikin wani shirin barkwanci mai suna ‘Imalu’ da yake wallafawa a shafinsa na YouTube mai suna ‘Dan’uwa TV‘. An ce...
Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar rage kaso 30 cikin 100 na sinadarin gishiri (sodium) a kowane nau’in abincin ɗan fakiti da ake sayarwa a kantuna da wuraren kasuwanci a kasar. Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin za ta soma aiwatar da wannan shirin ne a bana domin daƙile cutar hawan jini da dangoginta a ƙasar. Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano An kama sojoji 20 kan yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin lafiya kuma jakadiyar manufofin rage gishiri, Dokta Salma Ibrahim Anas, ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar shugaban kasa yayin bikin Ranar Abinci ta Duniya ta 2025 a Abuja. A cewarta,...
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Fulham, Alex Iwobi, na dab da kafa sabon tarihi a gasar Firimiya a matsayin ɗan wasan Nijeriya da ya fi buga wasanni a tarihin gasar. Idan Iwobi ya buga wasan da Fulham za ta kara da Arsenal a filin Craven Cottage yau Asabar, zai zama ɗan wasan Nijeriya na farko da ya kai buga wasanni 299 a Firimiya. A halin yanzu, Iwobi ya buga wasanni 298, inda yake daidai da tsohon ɗan wasan Newcastle United, Shola Ameobi, wanda ya riƙe wannan tarihin tsawon lokaci. Wannan zai kasance babbar nasara ga Iwobi wanda ke da shekaru 29 a duniya, tun da ya fara wasansa na farko a Firimiya ranar 27 ga watan Oktoba, lokacin da Arsenal...
Mai bai wa Gwamnan Filato shawara kan harkar tsaro, Janar Shippi Goshwe (mai ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnati tana ɗaukar sabbin ma’aikata ƙarƙashin Operation Rainbow domin inganta tsaron al’umma. Shugaban Ƙungiyar Matasan Berom (BYM), Barista Solomon Nwantiri, ya yi Allah-wadai da kisan tare da tambayar dalilin da ya sa ake amfani da zargin satar shanu a matsayin hujjar kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba. Waɗannan hare-haren sun ƙara jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da adalci domin kawo ƙarshen kashe-kashe a ƙauyukan Jihar Filato. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A...
Sayyidi Aliyu ya shaida hakan ne yayin jawabin bankwana da wayar da kan ɗaliban da suka samu gurbin karatun zuwa ƙasar Algeria na shekarar 2025, da ya gudana a cibiyar Sheikh Dahiru da ke Bauchi a ranar Litinin 13 ga watan Oktoba. Ya ce an ɗauki tsawon lokaci ana wayar da kan ɗaliban na tsawon shekara guda kan yadda za su kyautata rayuwarsu a can ƙasar da kuma samun ilimin da ake tsammani a garesu ba tare da matsaloli ba tare da koyar musu harsunan Farsanci da Larabci domin sauƙaƙa musu fara rayuwa a ƙasar Algeria. Ya yaba wa Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad bisa biyan kuɗin jirgi wa dukkani ɗaliban jihar su 50 daga cikin waɗanda za...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5. An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje. ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda. Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa. Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya...
A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka. Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa. ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar...
Gwamnatin Jihar Kano ta umurci Hukumar Hisba ta jihar da ta fara shirye-shiryen ɗaurin auren ma’aurata aƙalla 2,000 a ƙarƙashin shirinta na ɗaurin auren gata. Mataimakin babban Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen ya shaida wa kafar PUNCH a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Alhamis, inda ya ce nan ba da daɗewa ba hukumar za ta fara shirin don ganin an samu nasarar gudanar da taron bikin. An kama 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar Bayero “Muna shirin gudanar da ɗaurin auren wani rukunin ma’aurata guda 2,000 kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta umarta,” in ji shi. Duk da cewa, babban kwamandan bai bayyana ainihin...
An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato. Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo. Ya ce ’yan bindigar sun buɗe...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba. Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
Allah Ya yi wa fitaccen ɗan jarida a Jihar Kano Aliyu Abubakar Getso, rasuwa da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya. Abubakar Getso ya yi aiki a kafafen yaɗa labarai da dama da suka haɗar da na gwamnati da kuma masu zaman kansu. Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya da jikoki da dama. Iyalai sun ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Lahadi a gidansa da ke Second Gate a Unguwar Janbulo, Kabuga.
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”. Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya. Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar. “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta. Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja. Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu....
Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku: Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane...
Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.” Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki. A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin soma karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu waɗanda suka mayar da karuwanci sana’a. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce kuɗaɗen da masu sana’ar karuwanci ke samu za a riƙe cire musu haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji ta ƙasar. Oyedele ya yi wannan bayani ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a jiya Litinin, inda ya kawo misalan hanyoyin samun kuɗin da ake sanya wa haraji. Masanin harajin ya bayyana cewa sabbin dokokin ba su bambanta tsakanin hanyar halal ko ta haram wajen samun kuɗi ba — abin da suke dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga...
Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi. Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar da suka yi da Lesotho, inda Teboho Mokoena ya taka leda a ranar 21 ga Maris, 2025. FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace...
Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima NYSC. Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba. Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi...
Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari da ya danganci rajistar masu bautar ƙasa (NYSC) da manufofin hukumar da ke tattara bayanai kan ilimi wato NERD. A yanzu dai babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince don samun damar shiga ko samun hutu daga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) ba tare da kiyaye sharaɗin da NERD ta shar’anta ba. Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu A ƙarƙashin sabon tsarin wanda zai soma aiki daga 6 ga watan Oktoba, NERD ta wajabta cewa a yanzu rajistar ɓautar ƙasa tana ta’allaƙa ne da miƙa aikin binciken...
Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano Rahotanni sun ce ta fara ƙorafin cewa ba ta jin daɗin jikinta da alamu na rashin lafiya, inda daga daga bisani ta yanke jiki ta faɗi. Sai dai bayan an garzaya da ita asibitin gwamnati na Lapai, likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa. Fatima Adamu Muhammad,...
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba Bisa...
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka yi karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken...
Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki. Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira. Muna da yakinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.” Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Sanarwar ta ce an dakatar da wasu ƙarin mutum 8 da aka kama da laifuka masu nasaba da hakan tare da wanke ƙarin ɗalibai biyu daga zargin. Jami’ar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ɗaliban da aka kora sun aikata laifuka daban-daban da suka shafi karya ƙa’idojin jarrabawa. Cikin wadanda...
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ba shi da tushe balle makama, inda ta bayyana shi a matsayin mai cike da ruɗu da rashin inganci. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar “Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar bana, Premium Times ta tabbatar...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na Amuka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da...
Wani ɗalibi mai suna Ogbeche, ya kashe malaminsa Oshen, a makarantar sakandire da ke garin Ugboro, da ke Ƙaramar Hukumar Bekwarra a Jihar Kuros Riba. Rahotanni sun nuna cewa malamin ya yi ƙoƙarin raba faɗa tsakanin Ogbeche da wani ɗalibi. Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da fetur a farashin Naira Sai dai a fusace, ɗalibin ya fisge taɓarya daga hannun wata mata, ya buga wa malamin a kai, wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme. Duk da garzayawa da shi da aka yi zuwa asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwarsa. Wata ganau mai suna Lizzy ta ce: “Malamin kawai yaje rabon faɗa ne, amma Ogbeche ya fusata ya ɗauki taɓarya ya...
An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku da suka tsere, na fuskantar tuhuma kan laifin aikata lalata, wanda ya saba wa sashi na 259 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata da malaman makaranta na bogi 3,488 Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumba wani mai suna Yahaya Aliyu, mazaunin Tudun Jukun...
A wajen ɗalibin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, zane ba kawai sha’awa ba ce kaɗai, face hanya ta shiga kundin tarihin duniya. A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin zanen fuska. Kamfanin Indomie ne zai tallafa wa ɗalibin domin gwada bajintarsa wajen shiga kundin Guinness World Record. Burinsa shi ne zana fuskar mutane 12 ko sama da haka a cikin minti uku da kuma fuskar mutane 220 ko sama da hakan cikin sa’a guda, inda yake ƙoƙarin ƙwace kambun da Emilia Zakonnova, wadda ke riƙe da shi, wadda ta zana fuskar mutane 12 cikin...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Sanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ’yan sanda domin damfarar jama’a. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,...
Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno. Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka ɗaure mutum ɗaya shekaru 15 a gidan yari. Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya Sojojin da abin ya shafa sun haɗa da Raphael Ameh da Ejiga Musa masu muƙamin sajan, da kuma Patrick Ocheje mai muƙamin kofura. Binciken kotun ya nuna cewa Ameh ya karɓi sama da ₦500,000 daga harƙallar sayar da harsasai...
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba. Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna. An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere. Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin. Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da...