Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20
Published: 27th, November 2025 GMT
Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida.
Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na gaskiya ba ko kuma aka yi musu kwaskwarima.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai gayyaci Afirka ta kudu taron na badi ba, da Amurka zata karbi bakunci, kuma ya nanata sukar da yake yi wa Afirka ta kudun, kan zargin cewa an aikata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu a kan tsirarun fararen fata.
Amurka ta kauracewa taron na G20 na bana a Johannesburg, inda shugabanni suka amince da matakan da aka ayyana na magance matsalar dumamar yanayi da sauran matsaloli na duniya, duk da kin yardar Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi
Taron koli karo na 7 na tarrayar Turai da tarayyar Afrika, wanda aka bude a Luanda, na maida hankali kan batun diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi a karon farko.
A cewar ajandar taron, daya daga cikin manyan jigogi zai mayar da hankali kan diyya ta kudi da siyasa da ta shafi zaluncin mulkin mallaka da cinikin bayi, gami da lalacewar tattalin arziki, da al’adu da aka tara tsawon shekaru da dama.
Wannan lokaci ne da ba a taba ganin irinsa ba a wannan matakin siyasa: ba a taba sanya irin wannan batu a cikin ajandar taron da ya hada shugabannin kasashen Turai da Afirka ba.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta ware shekarar 2025 a matsayin shekarar “Adalci ga ‘Yan Afirka da kuma Mutanen da suka fito daga zuriyar Afirka ta hanyar diyya.
A cewar AllAfrica, kawai shigar da batun a cikin ajandar ya zama babban ci gaba, domin manyan biranen Turai sun dade suna guje wa batun.
Baya ga batun diyya, taron kolin ya yi magana kan batutuwa daban-daban: ci gaba mai dorewa, zuba jari, gyare-gyare ga tsarin kuɗi na duniya, rage raunin bashi, kirkire-kirkire, tsaro, da yanayi.
Kusan shugabanni 80 ne ke halartar taron, wanda João Lourenço, Shugaban Angola kuma Shugaban Tarayyar Afirka na yanzu, da António Costa, Shugaban Majalisar Turai, tare da Ursula von der Leyen suke jagoranta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci