NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki
Published: 24th, November 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative.
Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba.
NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka SaceShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da kuma halin da yake ciki a wannan lokaci.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro
Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan.
A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.
H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jiharWannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi.
PSUBEB ta sanar da cewa rufe makarantun mataki ne na wucin-gadi domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar lafiya da tsaron ɗalibai da muhimmanci.
Hukumar ta buƙaci Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi, shugabannin makarantu da shugabannin al’umma da su ba da cikakken haɗin kai wajen aiwatar da umarnin, tare da zama masu kula da duk wata alama ta rashin tsaro a yankunansu.