Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew
Published: 25th, November 2025 GMT
Tashar Talabijin ta Press TV ta Iran ta kaddamar da sabon sashenta na harshen Hebrew don isa ga masu sauraro na Yaren Hebrew na duniya.
Yanzu ana iya samun wannan sashen ta hanyar asusun X (@PresstvHebrew) da kuma tashar Telegram (@PresstvHebrew), kuma Za a kaddamar da cikakken shafin Intanet na tashar nan ba da jimawa ba.
Sashen na Hebrew zai rika bayar da labarai, binciken kwakwaf, da sharhi kan abubuwan da suke faruwa a yankin da ma duniya baki daya.
A cewar Ahmad Norouzi, darektan sashen watsa labarai a bangaren harsunan ketare na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB), ya bayyana cewa babban aikin tashar shi ne fallasa gaskiyar duk abinda jami’an Isra’ila ke neman boyewa, gami da takunkumin da aka sanya wa kafofin watsa labarai na yaren Hebrew a Isra’ila a lokacin rikice-rikicen baya-bayan nan.
Kaddamar da wannan tashar ya biyo bayan wani kuduri da Majalisar Koli ta Juyin Juya Halin a banagren Al’adu a Iran ta yi kwanan nan, wanda ya dora wa hukumar gidan talabijin da radiyo ta Iran (IRIB) alhakin kafa sashen sadarwa na talabijin na yaren Ibrananci ta duniya.
Tashar Talabijin ta Press TV ta bayyana cewa wannan shiri yana da nufin dakile farfagandar gwamnatin Sahayoniya da kafofin watsa labarai masu alaka da ita, don karfafa diflomasiyyar kafofin watsa labarai na Iran, da kuma gabatar da abubuwan da suka faru a yankin da kuma ra’ayin mutanen Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gagi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: watsa labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA)
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi Allah wadai da kudurin da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta amince da shi kwanan nan game da shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran.
Esmail Baghai ya yi wadannan kalamai ne a matsayin martani ga kudurin da Hukumar Gwamnonin IAEA ta amince da shi, wanda Faransa, Burtaniya, Jamus, da Amurka suka gabatar.
Ya bayyana cewa kudurin ya kara dagula batun nukiliyar Iran, maimakon taimakawa wajen warware shi.
Ya kara da cewa, “A ganina, abubuwan da ke cikin wannan kuduri ba su da wani tasiri ga wadanda suka tsara shi,” in ji shi.
Ya jaddada cewa kudurin, “ba wai kawai ya karya dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ayyukan IAEA na baya ba, har ma ya kasa yin wani nuni ga tushen matsalar, wato laifukan da gwamnatin Isra’ila da Amurka suka aikata a lokacin hare-haren da suka kai wa cibiyoyin nukiliya na Iran na lumana.”
Baghai ya bayyana cewa kudurin na IAEA ya fiddo a fili tsoma baki a cikin aikin IAEA kuma zai kara kawo cikas ga ‘yancin kai na hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.
Kudurin IAEA ya bukaci Tehran ta bayar da rahoto “ba tare da bata lokaci ba” game da tarin tacaccen sinadarin uranium dinta da kuma kayayyakin da aka lalata a lokacin harin Isra’ila da Amurka a watan Yuni.
A matsayin maida martani Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a watan Satumban da ya gabata don ci gaba da hadin gwiwa da IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu November 23, 2025 ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba November 23, 2025 An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci