An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
Published: 27th, November 2025 GMT
Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar Iran dangane da makaman guba wadanda Sadam Husain ya yi amfani da su a kan mutanen kasar a yakin shekaru 8 (1980-88).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron CWC a birnin Hague a ranar Talatan da ta gabata. Ya kuma kara da cewa Iran zata bukaci a hukunta kasashen da suka taimakawa Sadam Husain a wajen amfani da iran wadan nan makamai wadanda suka kashe kuma suka raunata Iraniyawa da dama.
Ministan ya isa birnin Haque ne a ranar Talata da safi don halattan taron na yaki da amfani da makaman guba ta kasa da kasa. A jawabinsa ya ce binciken da gwamnatin kasar Jamus ta yi a bayan, wanda ya tabbatar da laifi kan mutum guda bai wadatarba. Saboda akwai wasu kamfanonin da kum mai yuwa Jami’an gwamnatin kasar Jamus da dama a lokacin suna da hannu a cikin wannan babban laifin da aka aikata kan kasar ta Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025 November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Wani Kwamanda Na Mayakan Hizbullah
Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( a.s) daya daga cikin masu tafiyar gaskiya akan tafarkin jagorar matan duniya, dan’uwa, mujahidin Haisam Ali Tabtabai’ ya yi shahada, tare da wasu manyan kwamandoji sanadiyyar harin ‘yan sahayoniya.”
Dr.Ali Larijani ya kuma ce; Har yanzu Netanyahu yana ci gaba da tarbar aradu da ka, da hakan yake sake tabbatarwa da duniya cewa babu abinda ya kamata a yi sai kalubalantar wannan tsarin na ‘yan sahayoniya.”
A gefe daya, ma’aikatar harkokin cikin gidan Iran ta yi tir da wannan laifin na ta’addanci da ‘yan sahayoniya su ka tafka ta hanayr kai hari akan rukunin gidajen fararen hula a cikin Beirut wanda ya yi sanadiyyar shahadar babban kwamanda na gwagwarmata Haisam Tabtaba’i.
Bayanin na ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ya kuma ce: “Abinda makiya su ka yi, keta tsagaita wutar yaki ne da aka cimmawa a cikin watan Nuwamba na 2024, kuma hari ne na dabbanci akan kasar da take da shugabanci da hurumi.”
Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira da a hukunta jagororin wannan tsarin na ‘yan sahayoniya da ya aikata laifukan yaki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Kwamandan Jihadi Haisam al-Tabtabai November 24, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 162 November 24, 2025 Shugaban Kasa Ya Sami Halattar Makokin Shahadar Zahra (a) A Husainiyar Imam Khomani(q) November 24, 2025 Iran Da Omman Sun Tattauna Kan Al-Amuran Yankin Da Kuma Dangantaka Tsakaninsu November 24, 2025 Iran Ta Bukaci Daukar Matakan Da Suka Dace Kan Ta’asan Da HKI Ta Aikata A Beirut November 24, 2025 Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut November 24, 2025 Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno November 24, 2025 Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA) November 23, 2025 Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci