Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
Published: 26th, November 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000.
Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida.
Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu.
Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya, don tunatar da ku cewa gwamnatin Jihar Borno na alfahari da ku, wadda kan haka take saka hannun jari a kan makomarku.
“Kuna da muhimmanci ga ci gaba da sake gina jiharmu. Ilimin da ƙwarewar da kuke samu a nan zai amfani, ga jama’arku da kuma kannenku masu zuwa,” in ji Zulum.
Gwamna Zulum ya bayar da tallafin kuɗi na Naira 500,000 ga kowane ɗalibi, abin da ya jawo farin ciki matuƙa ga ɗaliban.
Daga nan, gwamnan ya tafi zuwa yankin Lucknow a ƙasar Indiya, inda ya yi irin wannan taimako ga ɗaliban Jihar Borno a Jami’ar Integral.
Ya kuma ba da umarni a bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatu na Jihar Borno da ke karatu a ƙasar Malesiya irin wannan tallafin kuɗi, yana mai jaddada alkawarin yin adalci ga dukkan ɗaliban da ke amfana da shirin tallafin karatu.
Ɗaliban sun yaba wa gwamnan saboda ziyarar, inda bayyana shi a matsayin shugaba mai tausayi da kulawa.
A cikin tawagar gwamnan akwai Babban Sakataren Fadar Gwamnatin Borno, Barista Mustapha Busuguma da Babban Sakataren Hukumar BOGIS, Injiniya Adam Bukar Bababe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno
Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan.
Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a KebbiYa ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa.
A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su.
Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu.
Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma ta koma gida a safiyar ranar Lahadi, amma sauran 12 har yanzu suna hannun maharan.
Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar yankin, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ceto ’yan matan cikin ƙoshin lafiya.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su ci gaba da yin addu’a, tare da sanar da hukumomi duk wani abun zargi.