Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji
Published: 23rd, November 2025 GMT
Rundunar Sojin Najeriya, ta ce barin jama’a da aka yi don su kare kansu ne ke rura wutar rikici a Jihar Filato.
Birgediya Janar MA Etsy-Ndagi, Shugaban Hulɗar Sojoji Da Fararen Hula ne, ya bayyana haka a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Jos.
An rufe duk makarantu a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin NajeriyaYa ce barin al’umma domin su kare kansu bai haifar da ɗai mai ido ba, illa ƙara tsananta rikice-rikice.
Jihar Filato na fama da rikice-rikice tun daga shekarar 2001, inda mutane da dama suka rasu, wasu kuma suka jikkata.
Wasu ƙungiyoyi a jihar sun yi kiran da a bar jama’a su kare kansu saboda yawan hare-hare da suke fuskanta.
Sai dai Janar Etsy-Ndagi ya ce rikici tsakanin manoma da makiyaya ya koma wani yanayi na ɗaukar fansa, inda kowane ɓangare ke kai wa juna hari.
Ya ce dole ne sojoji su ƙwace dukkanin makaman da ke hannun jama’ar gari domin kawo ƙarshen hare-haren ramuwar gayya.
A cewarsa: “Domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, dole mu tabbatar an ƙwace makamai daga hannun kowa, kuma babu wanda yake ƙera makami. Hakan ne zai ba da damar samun zaman lafiya.”
Ya ƙara da cewa: “Rikicin ya ɗauki wani sabon salo. Manoma suna zargin makiyaya da lalata musu amfanin gona, makiyaya kuma suna zargin manoma da satar musu shanu.
“Rikici na tsananta. Ba ma goyon bayan al’umma su kare kansu, muna kare jama’ar da ke fuskantar tashin hankali kuma muna ba su goyon baya.”
Ya kuma buƙaci mutanen jihar su zauna lafiya da juna tare da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankunansu.
Ya jaddada cewar Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da yaƙar matsalar tsaro a sassan ƙasar nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Makiyaya Tsaro su kare kansu
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF
Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa fiye da yara miliyan 400 a faɗin duniya na rayuwa cikin yanayin talauci mai tsanani.
A cikin sabon rahoton da ya fitar, UNICEF ya ce ƙarin ɗaruruwan miliyoyin yara na fuskantar hatsarin faɗawa talauci sakamakon katse tallafi, rikice-rikice, da kuma sauyin yanayi da ke gurgunta samun lafiya da walwala.
An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a JigawaRahoton ya nuna cewa yara miliyan 118 ba sa samun uku daga cikin muhimman buƙatun rayuwa guda biyar da suka haɗa da ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki, ruwa da tsafta, da kuma muhallin da ya dace.
Haka kuma, yara miliyan 17 na rasa fiye da huɗu daga cikin waɗannan muhimman buƙatu na yau da kullum da suka zama wajibi a ce suna samu a rayuwarsu.
UNICEF ta bayyana cewa mafi yawan yaran da ke cikin mawuyacin hali na zaune ne a ƙasashen Kudu da Saharar Afrika da kuma Kudancin Asiya.
A ƙasar Chadi kadai, rahoton ya ce kashi 64% na yara ba sa samun aƙalla biyu daga cikin ababen da suka zama dole a rayuwar yaro.
Rahoton ya kuma nuna cewa matsalolin tsafta na ci gaba da addabar yara a duniya, inda kashi 65% na yaran ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ba su da damar yin amfani da makewayi mai inganci, sai kuma wasu kashi 26 a ƙasashe masu matsakaicin tattalin arziƙi, da kuma kashi 11 a manyan ƙasashe, lamarin dake barazana ga lafiyarsu.
UNICEF ta danganta wannan yanayi da yawan rikice-rikice, tasirin sauyin yanayi, basuka da su ka yi wa ƙasashe katutu, da kuma yawaitar jama’a, lamarin da gaba ɗaya ke ƙara dagula rayuwar yara a faɗin duniya.