‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba
Published: 23rd, November 2025 GMT
A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin ba zata na ranar 7 ga Oktoba da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai.
Masu zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun taru, a dandalin Habima da ke Tel Aviv, suna sake nanata bukatarsu ta kafa kwamitin bincike da aka dora wa alhakin tabbatar da gaskiya da kuma cikakken bincike kan harin na Hamas (Operation Al-Aqsa Storm).
Tsohon Firaministan Isra’ila Naftali Bennett, madugun ‘yan adawa Yair Lapid, da MK Benny Gantz, Gadi Eisenkot, da Yair Golan suma sun halarci taron.
Masu shirya taron a cikin wata sanarwa sun ce yayin da majalisar ministocin Netanyahu ke “gudun neman kafa kwamitin binciken.
A cen baya, majalisar ministocin Netanyahu ta sanar da aniyyarta ta kafa “kwamitin bincike mai zaman kansa mai cikakken iko,” tare da kwamitin ministoci da aka dora wa alhakin gabatar da umarnin kwamitin cikin kwanaki 45.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba November 23, 2025 An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran November 23, 2025 An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka November 23, 2025 Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump November 23, 2025 Venezuela Ta Gargadi Amurka Kan Shirin Tada Hankali A Kan Iyakokin Kasar November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia
Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Habasha sun rattaba hannu ne akan yarjejeniyar aikin soja a tsakaninsa a wurin baje kolin jiragen sama na wannan shekara ta 2025 a birnin Dubai.
A bangaren Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya wakilce ta shi ne Janar Ibrahim Nasir al-Alawi, wanda wakilin ma’aikatar tsaro ne, sai kuma janar Rashid Muhammad al-Shamsi da shi ne kwamandan rundunar sojan sama.
A bangaren kasar Habasha kuwa wanda ya wakilce ta kuwa shi ne kwamandan rundunar sojan Saman kasar Laftanar janar Yilma Midasa Janaba.
Kasashen biyu dai suna da alaka a fagen aikin soja, da a shekarar 2019 ne su ka fara rattaba hannu akan yarjejeniyar aikin tare a wannan fagen.
A shekarar 2023 ma dai kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar fahimta juna da aiki tare a birnin Addis Ababa. Fagagen da wannan yarjejeniyar ta kunsa sun hada tattalin arziki, kai da komowar kudade, zuba hannun jari da kuma fada da ayyukan ta’addanci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran November 23, 2025 An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka November 23, 2025 Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump November 23, 2025 Venezuela Ta Gargadi Amurka Kan Shirin Tada Hankali A Kan Iyakokin Kasar November 23, 2025 CAN: Yawan Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ranar Jumma’a Sun Fi 300 November 23, 2025 Ribadu Ya Gana da Sakataren Yakin Amurka Kan Batun Kashe Kiristoci A Nijeriya November 22, 2025 Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki November 22, 2025 Isra’ila Ta Kashe Yara Falasdinawa Guda 22 A Yankin Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci