Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro
Published: 24th, November 2025 GMT
Gwamnatin Najeriya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu, wanda ya haɗa da samar da karin bayanan sirri, makamai da sauran kayan yaƙi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan Bayar da Bayanai da Tsara Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
Wannan dai ya biyo bayan jerin tattaunawa da aka gudanar a Washington tsakanin manyan jami’an Najeriya da na Amurka, domin zurfafa dangantakar tsaro da ƙulla sabbin hanyoyin haɗin gwiwa.
Tawagar Najeriya ƙarƙashin jagorancin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ta gana da jami’an majalisar dokokin Amurka, Fadar White House, ma’aikatar harkokin waje, da hukumomin tsaro na ƙasar.
A cikin tawagar akwai Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi; Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Leƙen Asirin Tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, tare da wasu wakilai daga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
A yayin ganawar, tawagar Najeriya ta ƙaryata zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar, tana mai cewa matsalolin tsaron ƙasar babu wanda suka ƙyale domin kuwa suna shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
Zargin na Trump ya haifar da ƙalubale da dama a cikin ƙasar, inda hannayen jari suka zube, baya ga ta’azzarar matsalolin da ake gani a ’yan kwanakin nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi.
A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare, tare da bayyana cewa ba da jimawa ba za a kuɓutar da ɗaliban cikin nasara, idan komai ya tafi yadda ake so.
An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEFYa nemi goyon bayan al’umma, yana mai cewa, “Haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci domin ganin an kammala wannan aiki lafiya lau, tare da dawo da yaran cikin iyayensu ba tare da wata matsala ba.”
A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan bindiga suka kai mummunan hari makarantar ta Maga, inda suka yi awon gaba da ɗalibai mata 25, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma musamman ma iyayen yaran.
Ministan ya ce tun bayan faruwar lamarin, Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin jami’an tsaro, ciki har da rundunar sojin sama da ta ƙasa, waɗanda ke aiki tare domin gano hanyar shiga ba tare da hallaka ko jikkata ɗaliban ba.
Ya ce, “Mun gano wurin da aka tsare yaran kuma da Yardar Allah za mu ceto su nan ba da jimawa ba. A yanzu haka muna a matakin ɗaukar tsattsauran mataki cikin hikima, domin tabbatar da cewa babu wata illa da za ta same su.”
“Ina kira ga al’ummar Kebbi da su ci gaba da haƙuri da kuma bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro. A irin wannan lamari, bayanan sirri daga jama’a na da matuƙar muhimmanci,” in ji shi.
Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a KebbiA bayan nan ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaron da ya koma Jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗaliban da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar.
Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace.
A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda ya bayyana umarnin a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis, ana sa ran Matawalle zai isa Birnin Kebbi da safiyar Juma’a.
“Yana da ƙwarewa sosai wajen fuskantar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023,” in ji sanarwar.
“A ranar 26 ga watan Fabrairu, 2021, ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 da 17 a makarantar kwana ta GGSSS Jangebe, Jihar Zamfara. ’Yan bindigar sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwar da su a ranar 2 ga watan Maris, 2021.”
Aminiya ta ruwaito cewa, shi ma dai Shugaba Tinubu ya ɗage tafiyarsa da aka tsara zuwa Johannesburg, Afirka ta Kudu, da Luanda a ƙasar Angola, domin ci gaba da samun rahotannin tsaro kan satar ɗaliban na Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a cocin Eruku da ke Jihar Kwara.