An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
Published: 27th, November 2025 GMT
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata sun kasa ficewa daga kasar bayan juyin mulkin.
Labarin ya kara da cewa sojojin da suka yi juyin mulkin sun kwace iko da kasar ne a dai-dai lokacinda ake irga kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Kafin juyin mulkin dai yan takaran shugaban kasa a zaben shugaba Umaro Sissoco da kuma Fernando Dias duk sun shelanta cewa su suka lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar.
Sojan da ya jagoranci juyin mulkin Denis N’Canha, wanda kafin haka mai gadin shugaban kasa ne, ya tsare shugaban kasar sannan ya bada sanarwan dakatar da duk wani al-amarin zabe, an rufe dukkan hanyoyin shiga ko fita kasar zuwa illa masha Allah. Jonathan dai ya je kasar ne a matsayin shugaban tawagar kungiyar kasashen yammacin Afirka a zaben shugaban kasa da kuma na majalisar dokokin da aka gudanar a ranar 23 ga watan Nuwamba da muke ciki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025 November 26, 2025 Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza November 26, 2025 Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da aka gudanar
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe.
Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu.
Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu.
Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan makon ma an kama mutane da dama, kuma ana tsare da su ne a cikin babban birnin kasar Kamfala.
Majiyar jam’iyyar hamayyar ta kuma ce, a ranar Litinin da aka bude yakin neman zabe kadai na kame mutane sun kai 100, sai kuma wani adadi mai yawa a jiya Talata.
Jami’an tsaron kasar sun sanar da kame mutane 7 bayan da su ka yi jefe-jefe da duwatsu a lokacin yakin neman zabe.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci