Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
Published: 26th, November 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan Nuwamba a jihar.
Shugaban Hukumar Kula Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar.
Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan.
Ya ƙara da cewa rigakafin watan Nuwamba za a gudanar da shi ne tare da Makon Lafiyar Uwa, Jariri da Yara (MNCH), inda ake ba mata masu juna biyu kulawar lafiya.
Dakta Sambo ya roƙi goyon bayan kafafen yada labarai domin isar da sako da kuma wayar da jama’a.
A nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Mohammed Rahama Farah, ya yaba wa jihar Jigawa bisa rage yawaitar cutar ta shan inna da kashi 58 bisa dari a shekarar 2024.
Sai dai ya yi gargadin ccewahar yanzu cutar na barazana a Najeriya , domin an samu lamura 72 a jihohi 14 a shekarar 2025, don haka akwai buƙatar ƙara faɗaɗa rigakafi.
Rahama Farah ya yi kira shugabannin kananan hukumomi da su sa ido sosai kan yadda ake gudanar da aikin domin tabbatar da nasara, tare da bukar kafofin watsa labarai su ƙara wayar da kai ga iyaye.
Ya kuma yi kira da a ɗauki aikin a matsayin na kowa da kowa domin kawo ƙarshen yaduwar cutar shan inna a Jigawa da sauran jihohin ƙasar nan.
Ita ma da yake jawabi a madadin Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Hajiya Firdaus Aminu ta yaba wa jihar bisa kyawawan shirye-shirye game da shirin yaki da cutar.
Za a gudanar da rigakafin shan innan na watan Nuwamba daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba, 2025.
Aikin, tare da makon MNCH, za su gudana ne ta hanyar ƙungiyoyi 2,015 na ma’aikatan wucin-gadi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan.
Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.”
“Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a Jihar Bauchi ya cancanci ya yi karatu a cikin yanayi mai aminci, kwanciyar hankali, kuma ba tare da tsoro ba.
“Saboda haka muna kira ga iyaye, masu kula, masu mallakar makarantu, da duk masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da kada su firgita, amma su kwantar da hankalinsu su kuma ba da haɗin kai.”
“Gwamnati tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don magance matsalolin cikin sauri da kuma cikakkiyar fahimta, tare da tabbatar da cewa ayyukan ilimi na yau da kullum, za su ci gaba da gudana da zarar an tabbatar da hakan.
“Muna kuma kira ga jama’a da su ci gaba da taka tsantsan. Idan kun ga wani abu da ba ku gane ba ku bayar da bayani wa jami’an tsaro saboda bayar da bayanai da a kan lokaci suna da mahimmanci wajen kare al’ummominmu.
“Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da samar da sabbin bayanai yayin da lamarin ke ci gaba.”