ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno
Published: 23rd, November 2025 GMT
Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan.
Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a KebbiYa ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa.
A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su.
Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu.
Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma ta koma gida a safiyar ranar Lahadi, amma sauran 12 har yanzu suna hannun maharan.
Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar yankin, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ceto ’yan matan cikin ƙoshin lafiya.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su ci gaba da yin addu’a, tare da sanar da hukumomi duk wani abun zargi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan mata awon gaba Farmaki Garkuwa hari ISWAP
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Asabar.
Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a NajeriyaYa bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar.
Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun kwana nan take har sai al’amura sun daidaita.
Gwamna Buni, ya roki jama’ar jihar da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya, inda kuma ya tabbatar da cewa gwamnati tana ɗaukar matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan mataki na zuwa ne biyo bayan sace ɗalibai da ’yan bindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja.
Yanzu dai matsalar na ci gaba da tayar da hankalin jama’a a Najeriya, inda mutane da dama ke kiran gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.