Daga Bello Wakili

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa matakan tsaron kasa.

A karkashin sabon umarnin, an bai wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ikon daukar karin jami’aaidubu ashirin,  wanda hakan zai kawo yawan sabbin  jami’an da za a dauka bana zuwa dubu hamsin.

Shugaban kasar ya kuma amince a yi amfani da sansanonin horas da matasa masu yi wa kasa  NYSC a matsayin wuraren horaswa na wucin gadi, sakamakon gyare-gyaren da ake yi a makarantun horar da ‘yan sanda a fadin kasar.

Haka zalika Jami’an da aka cire daga ayyukan tsaron manyan mutane za su samu horo na gaggawa kafin a tura su zuwa yankunan da ke da hadari.

Shugaban ya kuma bai wa Hukumar tsaro ta DSS umarnin gaggauta tura dakaru masu horo na musamman zuwa dazuka domin yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga. A don haka, hukumar ta DSS za ta dauki karin ma’aikata don karfafa wannan aiki.

Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su bada hadin kai ga matakan tsaron da ake dauka.

Ya yaba wa jami’an tsaro bisa ceto daliban Jihar Kebbi 24 da aka yi garkuwa da su, da masu ibada 38 a Jihar Kwara, tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da daliban da aka yi garkuwa da su a Jihar Niger da sauran wadanda ke tsare.

Shugaban ya umurci Rundunar Soji ta kara zafafa ayyuka a dukkan yankunan da ake rikici, tare da jaddada muhimmancin ladabi, gaskiya da kin amincewa da cin hanci ko sakaci.

Ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a hare-haren da suka faru a Kebbi, Borno, Zamfara, Niger, Yobe da Kwara, tare da karrama jaruman sojojin da suka rasa rayukansu, ciki har da Birgediya-Janar Musa Uba.

Shugaba Tinubu ya sake tabbatar da goyon bayansa ga jami’an saro na jihohi, tare da kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da ta fara nazarin dokokin da za su bai wa jihohin da ke son kafa ‘yan sandan jiha damar yin hakan.

Ya shawarci gwamnatocin jihohi su sake duba tsarin kafa makarantun kwana a wuraren da ke da nisa ba tare da wadatattun matakan tsaro ba, sannan ya yi kira ga cibiyoyin addini su kara inganta tsaron wuraren ibada.

Dangane da rikice-rikicen manoma da makiyaya, Shugaban ya bukaci kungiyoyin makiyaya da su rungumi tsarin kiwo na zamani (ranching) tare da yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya ta hannun sabuwar Ma’aikatar Raya Kiwo.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Dokar Ta Baci Tsaro Shugaban ya

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau

Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.

Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.

’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS

Wannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.

A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.

Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.

A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.

 

Cikakken rahoto na tafe…

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Tsaron makarantu: ’Yan Sanda da Shugabannin Makarantu sun tsara sabbin matakai a Gombe
  • Najeriya Ta Cimma Sabon Tsarin Hadin Gwiwa Kan Sha’anin Tsaro da Amurka