UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon
Published: 26th, November 2025 GMT
Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701.
“Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701 da kuma hurumin kasar Lebanon.” Inji shi.
Dakarun Masu Sanya ido kan zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon UNIFIL sun yi nazarin wurin kuma kuma tabbatar da cewa katangar ta ketare Layin da aka shata.
A cewar UNIFIL, sun gano cewa katangar tana cikin kasar Lebanon kuma ta kai kimanin mita murabba’i 4,000 a cikin kasar Lebanon”. Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa, tawagar ta sanar da sojojin na Isra’ila a hukumance game da keta dokar da suka yi, inda suka mayar da martanin cewa za su dubi lamarin.
UNIFIL ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin, da kuma ci gaba da Magana tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da cewa an kiyaye doka da kuma yin aiki da kudiri mai lamba 1701.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar.
Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari da ta kai a kudancin babban birnin Lebanon.
Haitham Ali Al-tabataba’i da aka fi sani da Abu Ali, ya yi shahada ne tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin beirut.
Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata.
Kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu.
Da yake bayyana hakan Shugaban Majalisar Zartarwa ta Hizbullah, Sheikh Ali Damoush ya ce duk lissafin Isra’ila game da kungiyar ya cutura, saboda ta yi imani da cewa kisan gillar manyan mutane da kwamandojin soja na kungiyar zai iya kai ta ga nasara in ji, a ranar Litinin.
“Irin wadannan kisan gillar suna karfafa kudurin kungiyar na fuskantar mamayar Isra’ila,” in ji shi yayin da yake jawabi a jana’izar Shahid Haytham Ali Tabatabai.
Ya yi wa Tabatabai godiya, yana mai jaddada cewa ya taka rawa a lokacin yakin farko na Hezbollah.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gagi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci