NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
Published: 25th, November 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita.
Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita.
Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan.
A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar Sikila a duniya. NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan cutar amosanin jini don gano yadda masu fama da ita ke ji a rayuwar su.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cutar amosanin jini
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro
Gwamnatin Najeriya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu, wanda ya haɗa da samar da karin bayanan sirri, makamai da sauran kayan yaƙi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan Bayar da Bayanai da Tsara Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
Atiku ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasuWannan dai ya biyo bayan jerin tattaunawa da aka gudanar a Washington tsakanin manyan jami’an Najeriya da na Amurka, domin zurfafa dangantakar tsaro da ƙulla sabbin hanyoyin haɗin gwiwa.
Tawagar Najeriya ƙarƙashin jagorancin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ta gana da jami’an majalisar dokokin Amurka, Fadar White House, ma’aikatar harkokin waje, da hukumomin tsaro na ƙasar.
A cikin tawagar akwai Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi; Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Leƙen Asirin Tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, tare da wasu wakilai daga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
A yayin ganawar, tawagar Najeriya ta ƙaryata zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar, tana mai cewa matsalolin tsaron ƙasar babu wanda suka ƙyale domin kuwa suna shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
Zargin na Trump ya haifar da ƙalubale da dama a cikin ƙasar, inda hannayen jari suka zube, baya ga ta’azzarar matsalolin da ake gani a ’yan kwanakin nan.