HausaTv:
2025-11-27@12:31:20 GMT

Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci

Published: 27th, November 2025 GMT

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa kasar a shirye take ta taimaka wa tarayyar Najeriya a fadan da take yi da ta’addanci.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha Maria Zakharova ce ta bayyana hakan, sannan kuma ta jinjinawa kokarin da gwamnatin ta Najeriya take yi a wannan fagen na kalubalantar masu wuce gona da iri.

Zakharova ta kuma ce, matsayar Rasha ba ta sauya ba akan yadda take kallon ta’addanci a matsayin barazana ga zaman lafiya na duniya.

Haka nan kuma ta ce, Rasha a shirye take ta bayar da taimako da kuma aiki tare da kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin MDD da kuma tarayyar Afirka.

Dangane da Najeriya, Zakharova ta kara da cewa; Rasha a shirye take ta ci gaba da bai wa Najeriya taimako, kuma sojoji da jami’an tsaron kasar suna da kwarewa mai yawa da su ka samu a fagen fada da ta’addanci.”

Haka nan kuma ta yi ishara da yadda fararen hula da su ka hada mata da yara suke jin jiki matuka saboda ayyukan ta’addanci.

Kasar Najeriya dai tana fama da matsalolin tsaro daga kungiyoyin ta’addanci da su ka hada Bokoharam, Iswap da kuma barayin daji masu garkuwa da mutane.

A cikin kasa da mako daya an sace daliban makarantun arewacin kasar da dama, da hakan ya tilastawa mahukunta rufe makarantu a jihohi masu yawa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sace ɗalibai: Idan Tinubu ba zai iya ba ya sauka kawai — PDP

Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu.

A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

“Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji Ememobong

Ya ci gaba da cewa, “Idan aka rufe makarantu, to ’yan ta’adda sun cimma nasara.”

Umarnin janye ’yan sanda daga faɗin manyan mutane na iya zama magana kawai —Shehu Sani Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC

Ya buƙaci gwamnati ta samar da tsari na musamman don magance matsalar tsaro, maimakon sauƙaƙa ta, ta hanyar rufe makarantu don kauce wa sace-sace da kuma neman yabo saboda siyasa.

Ememobong ya jaddada muhimmancin aiwatar da shirin samar da tsaro a makarantu, wanda ya ce ya ta’allaƙa ne kan bayanan sirri daga al’umma da kuma tsarin ɗaukar matakan gaggawa na dakile hare-hare.

Ya bayyana cewa rashin tsaro ya zama babban cikas ga ilimi a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar. Ya yi nuni da alƙaluman Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da ke nuna cewa Arewacin Najeriya na da mafi yawan yara da ba sa zuwa makaranta—miliyan 10.2 a matakin firamare da miliyan 8.1 a sakandare.

Ememobong ya ce, “Wannan bayanin ba wai kawai yana nuna mummunan hoto ba, har ma yana bayyana ainihin halin da ake ciki a Najeriya. Jerin hare-hare da sace-sace a jihohi daban-daban cikin mako guda na nuna yadda rashin tsaro ya zama sabon yanayin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin APC ta Bola Tinubu.”

Ya kuma soki yadda gwamnati ke mayar da martani ga sace-sacen ɗalibai, yana mai cewa, “Abin damuwa shi ne, duk lokacin da irin wannan mummunan lamari ya faru, martanin gwamnati ba ya da ƙarfi kuma ba ya nuna tausayi.

“Misali, maimakon Shugaban Ƙasa ya ziyarci jihohin Kebbi da Neja don jajanta wa iyayen da ’ya’yansu ke hannun ’yan bindiga da kuma karfafa jami’an tsaro, sai kawai ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro ya koma Kebbi.”

Ya ƙara da cewa kwatanta yadda aka tura tawagPDP ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.a zuwa Majalisar Dokokin Amurka da taron G-20 da kuma yadda aka tura wakili guda zuwa Kebbi, ya nuna yadda Fadar Shugaban Ƙasa ke ɗaukar wannan matsala da sakaci.”

PDP ta sake jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa shi ne babban aikin kowace gwamnati.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki
  • Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin
  • Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi
  • Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta
  • Sace ɗalibai: Idan Tinubu ba zai iya ba ya sauka kawai — PDP