Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
Published: 25th, November 2025 GMT
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare.
Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin.
A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniyar hadin kai domin kyautata rayuwar al’ummar kasar ta Yemen da kuma shimfida zaman lafiya.
A wani labari mai alaka da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta amabci cewa za a yi ganawa a tsakanin minista Abbas Arakci da takwaransa na Faransa Jean Noel Baro a gobe Laraba 26/ Nuwamba a birnin Paris.
Jigon tattaunawar shi ne bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma batun furusunonin Faransa da suke a Iran.
Haka nan kuma tattaunawar bangarorin biyu za ta tabo halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, sai kuma Shirin Iran na makamashin Nukiliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci Daukar Matakan Da Suka Dace Kan Ta’asan Da HKI Ta Aikata A Beirut
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bukaci a dauki matakan da suka dace kan HKI saboda yadda take keta hurumin kasashen yankin take kuma kara zubar da jinin mutanen yankin musamman kudancin kasar Lebanon da kuma hurumin gwamnatin kasar.
Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nnakalto Aragchi yana fadar haka a jiya Lahadi da yamma, inda ya yi allawadi da hare-haren da HKI ta kai kan unguwar Dhahiya ta birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiyan wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 5 da kuma raunatawa wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da daya daga cikin fitattun kwamandojin kungiyar Hizbullah Haytham Ali Tabatabai da wasu dakarun kungiyar su 4.
Mata da yara suna daga cikin wadanda suka ji rauni a wadan nan hare-hare. Wannan harion dai yana daga cikin daruruwan hare-haren da sojojin HKI suka kai kan kasar Lebanon tun bayan yarjeniyar tsagaita wuta na watan Nuwamban shekara ta 2024.
Aragchi ya gabatar da taziyyarsa ga kungiyar Hizbullah da kumaiyalan shahid Tabatabai ya kuma yayi kira da kungiyoyin kasa da kasa musamman MDD da kuma kwamitin tsaronta su dauki mataki a kan HKI saboda keta yarjeniayr watan Nuwamban shekara ta 2024.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut November 24, 2025 Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno November 24, 2025 Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA) November 23, 2025 Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu November 23, 2025 ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci