2025-11-24@18:56:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11916
«a kasar Pakistan»:
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon na juyayin shahadar kwamanda haitham Ali Al-tabataba’i da aka fi sani da Abu Ali wanda yayi shahada tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin berut na kasar labanon. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata, kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu. Kungiyar hizbullah ta bayyana cewa babban kwamandan ya bi dan uwansa da yayi shahada...
Dubban ‘yan Tunisia ne suka fito zanga-zangar lumana a babban birnin kasar kan abin da suka kira rashin adalci da danniya na wannan gwamnatin, yayin da suke zargin Shugaba Kais Saied da mulkin kama karya. Zanga-zangar ta kasance wani babban al’amari ne a baya-bayan nan da ya mamaye wasu bangarori a kasar wanda ya shafi ‘yan jarida, likitoci, bankuna, bangaren sufuri da sauran ababen more rayuwa. A watan da ya gabata, wasu fitattun kungiyoyin kare hakkin dan adam suka sanar da cewa hukumomi sun dakatar da ayyukansu saboda zargin suna karbar tallafin kudi daga wasu kasashen waje. Amnesty International ta ce murkushe kungiyoyin kare hakkin jama’a a kasar yana bukatar kawo dauki, yayin da gwamnati ke ci gaba da kama...
Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin bakin wake a hedkwatar FC dake peshavar na kasar Pakistan da safiyar yau kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 6, da ya hada da jamian tsaro 3 da kuma wasu guda 3 na daban, wannan shi ne hari mafi muni da aka kai kan jami’an tsaro a kasar Pakistan a wannan watan. Wannan harin yana nuna irin matsalar tsaro da kasar Pakistan ke fuskanta adaidai lokacin da ake samun karuwar ayyukan yan ta’adda daga kungiyar tehrik e Taliban TTP wadda Islamabad ke zarginta da gudanar da ayyuka a boye akan iyakar Afghanistan. Ana sa bangaren fira ministan kasar Pakistan Shehbaz sharif yayi tir da kai harin , kuma ya bukaci gudanar da bincike don...
Kakakin kungiyar Hamas yayi Tir da ci gaba da kai hare haren da Isra’ila ke yi a fadin yankin Gaza, yayi gargadin cewa wadannan matakai suna barazana sosai ga yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakaninta da Isra’ila a kasar masar a watan Jiya. A cikin wani bayani da Hazem qassem yayi gargadin cewa ci gaba da wuce gona da irin Isra’ila zai kai ga rusa yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakaninta da Isra’ila , kungiyar ta jaddada matsayinta na aiki da yarjejeniyar duk da ci gaba da keta ta da isra’ila ke yi. A wani bangare kuma akalla falasdinwa 4 ne suka yi shahada yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a yankin Gaza . sakamakon...
Ƙungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara kanana a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da sace-sacen mutane da ake kai wa wasu makarantu a arewacin kasar. Amnesty ta ce ta na nuna damuwa akan yadda gwamnatin Najeriya ke kara nuna gazawa a wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu musamman ma yara ‘yan makaranta. Isa Sanusi, shi ne daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa, abin da ke faruwa yanzu ya nuna cewa ilimi zai kara samun koma fiye da baya, sai dai bisa ga yadda abubuwa ke faruwa a yanzu na rashin tsaro da satar dalibai abin zai kara...
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin muscat na kasar Oman. Grundberg ya bayyanawa Araqchi ci gaban da aka samu kan batun kasar yamen kana yayi kira Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View...
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan. Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.” “Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a Jihar...
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya. A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane. A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali. Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan...
Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa mayaƙan sunyi wa matan kisan gilla ne bisa zargim yin shirka. Ƙungiyar ta kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya. An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar. Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen...
Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya. Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito. Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere A watan Nuwambar nan ne labaran ƙanzan kurege suka riƙa yaɗuwa cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya. Bayanai sun ce tun dai cikin watan Oktoban da ya gabata,...
Daga Bello Wakili Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawa da tawagarta ta yi da jami’an Amurka ta kara karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa domin kara kare ‘yan Najeriya. Tawagar, karkashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ta gana da manyan jami’an Majalisar Dokokin Amurka, Ofishin Bangaren Addini na Fadar White House, Ma’aikatar Harkokin Waje, Majalisar Tsaro ta Kasa da Ma’aikatar Yaki a birnin Washington DC A yayin tattaunawar, tawagar ta musanta zargin kisan kare dangi a Najeriya, tana mai jaddada cewa hare-haren da ake samu na shafar al’umma ne daga bangarori daban-daban na kabilu da addinai. Ta ce irin wannan kuskuren fassarar halin da ake ciki na haifar...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan Boko Haram sun file kan mata 2 a Borno Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78. Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18,...
Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13. A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan 13 da ke hannun ‘yan ta’addan, kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce, shugaban gundumar Huyum ya bayar da rahoto a ranar Asabar 22 ga Nuwamba cewa waxanda ake zargin mayaƙan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace ‘yan matan, yayin da suke aiki a wata gona a gundumar Mussa. Tawagar ’yan sanda, sojoji, Sibiliyan JTF, da mafarauta da ’yan banga nan da nan suka fara...
Daga Ali Muhammad Rabi’u Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara ta sanya ranar 1 gawatan Disamba a matsayin wa’adin karshe na biyan kudin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya jaddada cewa babu tabbaci yiwuwar karin wa’adi. Sanarwar ta ce hukumar za ta tura kudaden Hajji ga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) domin cika wa’adin da Hukumar Hajjin Saudiyya ta gindaya. Haka kuma ta tabbatar da cewa fara aikin visa wato takardar izinin shiga kasar Saudiyya zai kasance a watan Fabrairu 2026, kuma duk wani jinkiri na iya hana maniyyaci samun damar zuwa aikin Hajjin na 2026....
Mahukunta a tarayyar Nigeria sun sanar da cewa a tsakanin kananan yara 303 na makarantar Majami’ar Roman Katolika da aka sace a jihar Niger, 50 daga cikinsu sun gudu, sun kuma isa wurin iyalansu. Masu tafiyar da makarantar ne su ka sanar da hakan a jiya Lahadi tare da kara cewa shekarun yaran da su ka gudu shekarunsu suna a tsakanin 10 ne zuwa 18. Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a jihar Niger, Rev. Busul Dauwa Yohanna ne ya sanar da haka, sannan ya kara da cewa: “A halin yanzu da akwai sauran raya 253 da malamai 12 da basu satar mutanen suke rike da su.” A gefe daya shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinibu ya sanar da tseratar da...
Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen. Masana ilimin kasa sun ce lokaci na karshe da dutsen ya yi aman wuta shi ne shekaru 10,000 da su ka gabata. Bugu da kari, masana ilimin kimiyya sun ce abinda ya faru yana da jan hankali bisa la’akari da cewa a ya dade bai yi amanwuta ba. Shi dai dutsen Hayli Gubbi yana da nisa kilo mita 15 daga dutsen Etra Ali wanda shi ma yana yin aman wuta. Yankin da lamarin ya faru wanda ake kira da “Dankali”yana daga cikin wuraren da su ka fi tsananin zafi a duniya da ba kasafai bil’adama...
Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara, Gwoza (Borno), bayan sun zarge su da yin shirka. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ƙungiyar kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya. An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar. Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen asiri, ko kuma yunkurin tserewa. Sace ɗalibai: Idan ba zai iya...
Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( a.s) daya daga cikin masu tafiyar gaskiya akan tafarkin jagorar matan duniya, dan’uwa, mujahidin Haisam Ali Tabtabai’ ya yi shahada, tare da wasu manyan kwamandoji sanadiyyar harin ‘yan sahayoniya.” Dr.Ali Larijani ya kuma ce; Har yanzu Netanyahu yana ci gaba da tarbar aradu da ka, da hakan yake sake tabbatarwa da duniya cewa babu abinda ya kamata a yi sai kalubalantar wannan tsarin...
A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Lahadi ta ce; “A cikin dukkanin alfahari Hizbullah tana sanarwa da ‘yan gwgawarmaya da al’ummar Lebanon, shahadar babban kwamanda na jihadi Shahid Haisam Ali Tabtaba’i ( Sayyid Abu Ali) wanda ya yi shahada sanadiyyar harin wuce gona da iri na yaudara na Isra’ila a yankin Harrik dake unguwar Dhahiya a kudancin Lebanon.” Sanarwar ta kuma kara da cewa; Shahidin ya hade da ‘yan’uwansa shahidai bayan tsawon lokaci na jihadi,gaskiya, kyakkyawar niyya da tsayin daka akan tafarkon gwgawarmaya da aikin da babu kakkautawa wajen fuskantar abokan gaba mhar zuwa lokaci na karshe na rayuwarsa.” Haka nan kuma sanarwar ta ci gaba da cewa; Shahidin yana cikin wadanda kafa harsashin gwgawarmaya saboda...
Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya. A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane. A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali. Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan...
Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun sakandaren kwana a matsayin wani mataki na kariya ga ɗaliban makarantun. A cikin wata sanarwa da Mamman Mohammed, kakakin gwamnan, ya ce, wannan shawara ta biyo bayan taron tsaro tsakanin Gwamna Mai Mala Buni da shugabannin tsaro a jihar, inda suka yi nazari kan abubuwan da suka faru na tsaro a makarantu a wasu sassan ƙasar nan. Sanarwar da Babban Sakatare na ma’aikatar Ilimi na Jihar, Dakta Bukar, ya sanya wa hannu, ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana nan take har sai an samu ci gaba a lamarin. Gwamna Buni ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi wa shugabanni, jami’an tsaro, addu’ar ci-gaba da samun zaman lafiya...
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da makarantun Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan. Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.” “Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a...
A dare na uku na makokin shahadar Fatiman Azzahra (s) diyar manzon All.. (s) shuwagabannin bangarorin gwamnati 3 a nan Iran sun sami halattan makakinta (s) a Husainiyyar Imam Khomanin(q) dake nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasa Dr Masoud Pazeshkiya, Alkalin alkalai Hujjatul Islam Sheikh Ibrahim Ijeyi da kuma Muhammad Bakir Qalibaf sun sami halattan taron makoki da ta’ayin Zahra, wanda Hujjatul Islam Nasir Rafi’ii ya karanta. A cikin jawabinda a zaman makokin Rafi’ii ya yi maganar Jagoranci, da kuma yadda Zahra (s) ta yi amfani da ragowar rayuwarta dan kadan bayan shahadar Mahaifinta don assasa wata harka ta goyon bayan hakkin mijinta kuma shugabanta Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib(a). Harka wanda zai...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo al-amura da suka shafi halin da ake ciki a yankin musamman HKI da kasashen yankin, da kuma dangane da kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Ommam ta taka rawar a zo a gani a kokarin kasar Iran na kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma shiga tsakanin Iran da kasashen yamma dangane da shirin kasar na makamashin Nukliya. Ziyarar da Aragchi ya kai Muscat dai yana daga cikin shirin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na tuntubar kasashen makobta...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bukaci a dauki matakan da suka dace kan HKI saboda yadda take keta hurumin kasashen yankin take kuma kara zubar da jinin mutanen yankin musamman kudancin kasar Lebanon da kuma hurumin gwamnatin kasar. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nnakalto Aragchi yana fadar haka a jiya Lahadi da yamma, inda ya yi allawadi da hare-haren da HKI ta kai kan unguwar Dhahiya ta birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiyan wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 5 da kuma raunatawa wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da daya daga cikin fitattun kwamandojin kungiyar Hizbullah Haytham Ali Tabatabai da wasu dakarun kungiyar su 4. Mata da yara...
Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar Hizbullah Shahid Ali Tabatabai. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyoyi da kasashen da suka yi allawadai da hare-haren kamar haka. Akwain kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, PFLP, kungiyar falasdinawa masu gwagwarmaya (PMM), Ansarullah mai gwagwarmaya. Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen JMI da kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki duk sun yi allawadai da hare-haren sun...
Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara da cewa ISWAP ta kama wadan nan yan mata wadanda suke da shekaru tsakanin 13-19 ne a lokacinda suke aiki a gonakinsu a gundumar Mussa na karamar Hukumar ta Askira. Jaridar ta kara da cewa wannan satar yan mata da yan makaranta ya biyo bayan irinsu da suka yi a makarantar mata ta Maga a karamar hukumar Wasagu na jihar Kebbi da kuma na makarantar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar da ayyukan ƙasa. Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar sojin sama, da na ƙasa da na ruwa da Darakta Janar na ma’aikatar tsaro ta DSS da kuma Sufeto Janar na ƴansanda Kayode Egbetokun. Sanarwar ta ce, daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa to ya nemi...
Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare. Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. ’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi Onanuga, ya ce daga yanzu ’yan sanda za su mayar da hankalinsu ne aikin kare al’umma da yaƙar ’yan ta’adda. An ɗauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, wanda manyan shugabannin tsaro suka halarta, ciki har da shugabannin ’yan sanda, sojin sama, sojin ƙasa da hukumar DSS. Sabon tsarin ya nuna cewa duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro dole ne,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi. Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba. Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a. Ta kuma ce ta...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN “‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.” Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.” Ya bayyana ’yan...
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi Allah wadai da kudurin da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta amince da shi kwanan nan game da shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran. Esmail Baghai ya yi wadannan kalamai ne a matsayin martani ga kudurin da Hukumar Gwamnonin IAEA ta amince da shi, wanda Faransa, Burtaniya, Jamus, da Amurka suka gabatar. Ya bayyana cewa kudurin ya kara dagula batun nukiliyar Iran, maimakon taimakawa wajen warware shi. Ya kara da cewa, “A ganina, abubuwan da ke cikin wannan kuduri ba su da wani tasiri ga wadanda suka tsara shi,” in ji shi. Ya jaddada cewa kudurin, “ba wai kawai ya karya dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ayyukan IAEA...
Ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin Isra’ila a Kudancin babban birnin Kasar, inda kuma ta raunata kimanin fararen hula 28. A cewar ofishin Firayim Minista Benjamin Netanyahu, harin an kai shi kan “babban hafsan sojojin Hezbollah,” Ali Tabataba’i, wanda Isra’ila ke zarginsa da “jagorantar ƙarfafawa da kuma ba da makamai” ga kungiyar. Shugaban Lebanon Michel Aoun ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa ya nuna rashin halin ko kula da gwamnatin Tel Aviv ke yi wa kiraye-kirayen kasashen duniya na dakatar da keta haddi a kasar Lebanon. Ita ma kungiyar Jihadin Musulunci ta Falasdinu ta yi Allah wadai da harin, tana mai daukar alhakin al’ummar duniya. An ruwaito...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa an ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara. Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kubutar dalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja. “Godiya ga jami’an tsaronmu a ‘yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara,” in ji shi. Sai dai ba yi karin bayani ba kan yadda aka ceto su. “Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a kasa baki daya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan...
A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin ba zata na ranar 7 ga Oktoba da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai. Masu zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun taru, a dandalin Habima da ke Tel Aviv, suna sake nanata bukatarsu ta kafa kwamitin bincike da aka dora wa alhakin tabbatar da gaskiya da kuma cikakken bincike kan harin na Hamas (Operation Al-Aqsa Storm). Tsohon Firaministan Isra’ila Naftali Bennett, madugun ‘yan adawa Yair Lapid, da MK Benny Gantz, Gadi Eisenkot, da Yair Golan suma sun halarci taron. Masu shirya taron a cikin wata sanarwa sun ce yayin da majalisar ministocin...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara. ’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka da Kogi a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji A cikin wani sako da Tinubu ya wallafa a X a ranar Lahadi, ya ce yana bibiyar yanayin tsaro a fadin kasar nan, kuma zai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kare ’yan Najeriya. An yada bidiyon...
Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan. Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a Kebbi Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa. A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su. Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu. Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma...
Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na kuɗi tare da dukkan manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin jihar. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Ilimi na Gaba da Sakandare Alhaji Issa Abubakar-Tunga da Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Dakta Halima Bande, a Birnin Kebbi. Kwamishinonin sun bayyana cewa rufe makarantun gwamnati da na kuɗi a jiha ya zama dole sakamakon hare-haren da aka kai a wasu sassan jihar kwanan nan. Sun lissafa makarantun gaba da sakandare da abin ya shafa kamar haka: Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero da Kwalejin Kimiyyar...
Ɗalibai 50 da aka sace a Makarantar St. Mary’s da ke garin Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, sun tsere daga hannun ’yan bindiga. ’Yan bindigar da suka sace su, sun kai hari makarantar da safiyar ranar Juma’a. Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji An rufe duk makarantu a Kebbi Maharan sun harbe mai gadin makarantar sannan suka sace ɗalibai sama da 200 da ma’aikatan makaranta 13, ciki har da malamai. A farko, Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Jihar Neja, Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, ya ce ɗalibai 215 tare da ma’aikata 12 aka sace. Sai dai a ranar Asabar, ya ce har yanzu ba inda ɗalibai 88...
Rundunar Sojin Najeriya, ta ce barin jama’a da aka yi don su kare kansu ne ke rura wutar rikici a Jihar Filato. Birgediya Janar MA Etsy-Ndagi, Shugaban Hulɗar Sojoji Da Fararen Hula ne, ya bayyana haka a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Jos. An rufe duk makarantu a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya Ya ce barin al’umma domin su kare kansu bai haifar da ɗai mai ido ba, illa ƙara tsananta rikice-rikice. Jihar Filato na fama da rikice-rikice tun daga shekarar 2001, inda mutane da dama suka rasu, wasu kuma suka jikkata. Wasu ƙungiyoyi a jihar sun yi kiran da a bar jama’a su kare kansu saboda yawan hare-hare da suke...
Taron na kasar Brazil akan muhalli wanda shi ne karo na 30 ya amince da bayar da tallafin kudade ga kasashe masu karancin kudaden shiga domin fuskantar matsalar dumamar yanayin duniya. Mahalarta taron da su ka fito daga kasashen duniya mabanbanta, wadanda suke fafutukar ganin an shawo kan matsalar da ake fuskanta a duniya ta sauyin yanayi. Sai dai kuma bayanin da aka fitar bai yi Ishara da tasirin makamashin man fetur da dangoginsa a matsayin wadanda suke taka rawa wajen gurbata yanayin duniya. Sabanin da aka sami a tsakanin tarayyar turai da kuma kasashen larabawa masu arzikin man fetur ne ya sa aka jinkirta yin magana man fetur din da dangoginsa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin kasuwanci da ake da shi a tsakanin kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa wanda ya kamata a san yadda za a magance shi. Antonio Gutrres ya kuma ce: “Wani abu guda daya wanda zan iya bayar da tabbaci a kansa shi ne cewa ofishin babban magatakardar MDD zai yi duk abinda zai iya yi domin yin gyara a cikin rashin daidaito da...
Shugabannin kasashen duniya da su ka halarci taron kungiyar G 20 sun amince da kudurin akan hanyoyin bunkasa tattalin arziki, sai dai ba a fitar da da cikakken bayani akan abinda ya kunsa ba. Gwamnatin Donald Trump ta ki halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude jiya a kasar Afirka Ta Kudu, da kuma yake zuwa karshe a yau Lahadi,sannan kuma ta yi kira da kar a kuskura a fitar da wani kuduri ba tare da wakilanta suna wajen ba. Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa; Amincewa da kudurin wani sako ne akan cewa duniyar da bangarori mabanbanta suke tafiyar da ita, za ta iya daukar matakai.” A baya kadan shugaban kasar Afirka ta...
Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Habasha sun rattaba hannu ne akan yarjejeniyar aikin soja a tsakaninsa a wurin baje kolin jiragen sama na wannan shekara ta 2025 a birnin Dubai. A bangaren Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya wakilce ta shi ne Janar Ibrahim Nasir al-Alawi, wanda wakilin ma’aikatar tsaro ne, sai kuma janar Rashid Muhammad al-Shamsi da shi ne kwamandan rundunar sojan sama. A bangaren kasar Habasha kuwa wanda ya wakilce ta kuwa shi ne kwamandan rundunar sojan Saman kasar Laftanar janar Yilma Midasa Janaba. Kasashen biyu dai suna da alaka a fagen aikin soja, da a shekarar 2019 ne su ka fara rattaba hannu akan yarjejeniyar aikin tare a wannan fagen. A shekarar 2023 ma dai kasashen biyu...
Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun sakandire na gwamnati da na masu zaman kansu nan take. Haka kuma, gwamnatin ta rufe dukkan manyan makarantun gaba da sakandire a faɗin jihar, banda Kwalejin Nazarin Aikin Jinya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi. An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, tare da Kwamishiyar Ilimin Firamare da Sakandare, Dokta Halima Bande, suka fitar a Birnin Kebbi, ranar Lahadi. Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon barazanar hare-haren da ake samu a...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana adawarsa da duk wani mataki da zai iya kara tada hankali, musamman hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Lebanon, yana mai jaddada “wajibcin janyewar sojojin mamaye.” Wannan ya zo ne a cikin sakon taya murna da Pezeshkian ya aika wa Shugaban Lebanon Joseph Aoun a ranar ‘Yanci, inda ya nuna godiyarsa ga al’ummar Lebanon da kuma fatansa na “lafiya, kwanciyar hankali, da wadata.” A cikin sakonsa, Pezeshkian ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da Lebanon, jama’arta da gwamnatinta, kuma manufofinta marasa tabbas shine tallafawa kwanciyar hankali, wadata, da kuma zama tare tsakanin dukkan al’ummomin Lebanon. Ya kara da cewa Tehran na fatan “haɓaka haɗin gwiwa da dangantakar kasashen...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission Substation da ke Owerri, Jihar Imo, lamarin da ya janyo fargaba da tayar da hankali ga ma’aikatan da ke wurin. Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na ƙasa ya fitar, NUEE ta ce wannan hari na...
161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda wasu...
Ministan ayyukan leken asiri na kasar Iran Esma’il Khatib ya bayyana cewa HKI na fuskantar ayyukan leken asiri mafi muni a tarihin samauwar haramtacciyar kasar, kuma a halin yanzun Jami’an tsaron HKI da dama suna aikin leken asiriwa wa JMI, musamman bayan da gwamnatin yahudawan ta bada sanarwan kama wani sojan rundunar sama ta kasar saboda aiki leken asiri wa JMI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Khatib yana fadar haka a jiya Asabar a wani ziyarar aiki da ya kai lardin Kokulue Boye Ahmad a kudancin kasar. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun bada sanarwan cewa, sun tabbatar da cewa laifin aikin leken asiri wa kasar Iran kan wani sojan sama na kasar dan...
Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi. Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana gabatar da jawabi bayan taron shuwagabannin na G20 na kwanaki 2. Ramanposa yace kungiyar G20 ba zata taba manta da sauyin yanayi ba, kuma ba zata kyala sauran kasashen duniyaba ba, kuma kungiyar zata yi kokarin ganin ta daga sauran kasashe raunan a duniya zuwa matsayin da ya dace na tattalin arziki. Kakakin Ramanposa ya ce dukkan kasashen da suka halarci taron sun amince da jawabin bayan taron. Amma shugaban...
Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a...
Gwamnatin kasar Venezuela ta gargadi kasar Amurka kan duk wani shirin kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro, a dai-dai lokacin da gwamnatin Trump take bada wani sabon yunkuri nan kusa na ganin ta kwace iko da kasar Venezuela, ta kuma raba Madoro da shugabancin kasar. Kafafen yada labarai da dama sun nakalto manya-manyan Jami’an gwamnatin shugaba Trump suna fadar cewa sojojin kasar suna shirin kaddamar da hare-hare kan kasar Venezuela nan ba da dadewa ba, don ganin sun kwace ikon kasar daga hannun shugaba Madoro. Sai dai mamu sanya ido a kan abubuwan da ke faruwa a kusa da kasar Venezuela sun bayyana cewa, gwamnatin Amurka ta tura kataparen jiragen daukar jiragen yaki wato Carier, da wasu jiragen yawan yaki...
A dai-dai lokacinda matsalolin tsaro suke kara tarbarbarewa a arewacin tarayyar Najeriya, kungiyar kiristoci ta kasa wato CAN ta bada sanarwan cewa yawan yaran da aka sace a ranar Jumma’an da ta gabat a makarantar St Mary a unguwar Papiri na karamar hukumar Agwara a jihar Naija ya kai 303. Daga cikin wadanda yan bingida suka sace har da malaman makarantar 12. Jaridar Premiumtimes ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar Can a jihar Bulus Yohanna yana cewa sun tabbatar da wannan labarin ne a binciken da suka gudanar a makarantar. Yohanna yace “Jimillar yan makaranta 303 ne aka sace, tare da malamansu 12, sannan wasu 88 da suka yi kokarin tserewa duk an kama su an tafi da su. Ya...
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi. A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare, tare da bayyana cewa ba da jimawa ba za a kuɓutar da ɗaliban cikin nasara, idan komai ya tafi yadda ake so. An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF Ya nemi goyon bayan al’umma, yana mai cewa, “Haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci domin ganin an kammala wannan aiki lafiya lau,...
Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan. A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025. H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar Wannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi....
Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, kan yawaitar ambaliya a yankin. Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya A cewar Injiniya Bichi, “Mun karɓi kokenku hannu biyu. Matakin da shugabancin Jahun ya ɗauka ya yi dai-dai. Za mu tura ƙwararrun injiniyoyi su yi aikin da ya kamata domin daƙile ambaliyar, tare da inganta noman yankin...
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan. Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Asabar. Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Ya bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar. Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi. ’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalolin tsaro masu yawan gaske, amma tana aiki tuƙuru don magance su. Ya yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba idan al’ummarta suka ci gaba da fuskantar hare-hare, talauci, da tsoro. “Ba abin da ke damuna kamar...
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki da gaggawa da Nijeriya wajen rage hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi. Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke kara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da kungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a kauyuka, da...
Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki
Rahotanni sun bayyana cewa daliban jami’ar St Gorges dake London sun yi zanga-zangar nuna adawa da daukar wani farfesa a fanni tattalin arziki kuma tsohon sojan Amurka aiki a makarantar, inda suka nuna kasancewarsa babban barazana ne ga dalibai musamman ga falsdinawa da kuma masu nuna goyon bayansu. Masu zanga-zangar sun bayyana cewa daukar tsohon sojan isra’ila aiki yana Isar da wani mummunan sako ne ga dalibai kai tsaye musamman wadanda suka shafi rikicin dake faruwa a yankin gaza, kuma matakin da jamiar ta dauka yayi karo da alkawuran da ta dauka na bada ilimi da kuma kare hakkin dan adam. Akalla dalibai magoya bayan falasdinawa fiye da 100 ne da magoya bayansu suka yi gangami a wajen jami’ar da...
Sojojin Isra’ila sun kashe wasu yara falasdinawa guda biyu a yankin gaza duk da yajejejeniyar dakatar da bude wuta da a sanya hannu akai, da ta fara aiki a farkon watan oktoba kamar yadda hukumar unicef tayi gargadi akai. Tun da aka rattaba hannun kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ranar 11 ga watan oktoba, akall yara dubu 67 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren isra’ila a yankin Gaza, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, wannan shi ne kididdigar da aka fitar dake nuna cewa kullum isra’ila na kashe yara biyu a kullum Kakakin hukumar kula da kana nan yara na majalisar dinkin duniya yayi gargadi game da matsanancin halin dubban daruruwan yara falasdinawa za su shiga...
Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sunan brigadier janar Ali Jahanshashi a matsayin sabon kwamandan dakarun sojan kasar iran inda ya gaji brigadier janar Kiumars Haidari Bayanan da yayi jim kadan bayan sanar da nadin nasa a yau Asabar, Jahanshahi ya jaddada cewa dakarun sojin kasar a shirye suke su mayar da martani kan duk wata barazana ta hanyar amfani da kwarewarsu da makamai na zamani da kuma daukan darasi kan rikicin da ya faru abaya bayan nan musamman yakin kwanaki 12 da Israila ta kallafa mata. Haka zalika ya kara da cewa a halin yanzu sojoji sun bada fifiko ga kaidoji da dokoki guda 5 da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah imam khamnai ya sanya, wanda suka...
Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale. ‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware shekaru da dama don Shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe School Programme), a yayin da ake sake nuna damuwa cewa makarantun Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin hadari, inda a baya-bayan nan aka sace ‘yan mata a Jihar Kebbi. Wadannan kudurori sun biyo bayan tayin da Sanata Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi North) ya gabatar, wanda ya yi...
Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi yunkurin sacewa, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar mata 10 da yara 15 domin tafiyada su. Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau. Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali. Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja A yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa. Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa. Sun...
Daga Aliyu Lawal Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar sakamakon sace dalibai da aka yi a Makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Karamar Hukumar Agwara. Gwamna Mohammed Umar Bago ne ya sanar da hakan a Minna bayan wata tattaunawar tsaro gaggawar ta da aka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki. Ya ce matakin ya zama wajibi domin kare rayukan dalibai yayin da ake kara kokarin ceto yaran da aka sace. Gwamna Bago ya jaddada cewa yanzu lokaci ne na daukar mataki a maimakon zargin juna, inda ya bayar da umarnin cewa a rufe...
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro. Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba. Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar...
Daga Isma’il Adamu Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati, da na masu zaman kansu a fadin jihar biyo bayan kalubalen tsaro da ya addabi makarantun kasar nan. Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu hare-haren sace ɗaliban makarantu da suka faru a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, Sani Danjuma, ya sanyawa hannu, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin nuna jajircewar gwamnati wajen kare ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu. Sanarwar ta ce duk da cewa rufe makarantun na iya kawo cikas ga iyaye da ɗalibai, tsaro ya fi komai muhimmanci yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro a...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya ce Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa za a mayar da rarar kuɗin ne ga maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu a fadin jihar kafin a sanar da rage kudaden. Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta bayyana sabon farashin cewa yankin Arewa zai biya sama da Naira Miliyan 7.6, yayin da waɗanda za su tashi daga yankin Kudu za su biya sama...
Hukumar Kula da Tsaftace Muhalli da Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA) ta ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a na watannin ƙarshen shekara na shekarar 2025 a Tashar Motoci ta Malam Nasiru El-Rufa’i da ke ’Yan Ƙarfe, Sabon Gari, Zariya. Taron yaƙin wayar da kan jama’a na ‘Watannin Ember’ na shekarar 2025 mai taken: “Tafiyar aminci ana cimma ta ta hanyar tuƙi cikin tsaro,” ya samu halartar hukumomin tsaro daban-daban da ke da ƙudirin rage haɗurra a kan manyan hanyoyin jihar A wajen taron, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya jaddada muhimmancin rawar da kowa a cikin al’umma zai taka wajen tabbatar da tsaron hanya da kuma tuƙi cikin natsuwa. Wakilin Sarkin a taron, Injiniya Ibrahim Balarabe Musa, ya...
A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin. Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari Bizo yana nuna jin dadinsa da komawar shugaban kasar sannan ya kara da cewa, batun gina kasa da hadin kan al’umma shi ne abinda suke son ganin ya tabbata.” A tsawon lokacin da yake rangadin, shugaban kasar ta Nijar ya yi kira ga al’umma da su zama masu tsayin daka,su kuma sojoji su kasance masu zama cikin fadaka da sa ido. Ana daukar wannan ziyarar...
Shugaban bangaren sandarwa da bayanai na gwamnatin Afirka Ta Kudu, William Bawli ya ce; rashin zuwan Amurka taron kungiyar G 20 da ake yi a kasar babu wani tasiri da zai yi. William ya kuma ce, idan Amurkan ta sauya ra’ayinta za ta iya zuwa kuma ana maraba da ita. Shugaban bangaren sadarwar na gwamnatin Afirka Ta Kudu, ya fadawa kamfanin dillancin labarun “Sputnik” na Rasha cewa; Tun daga lokacin da kasar ta Afirka Ta Kudu ta karbi jagoracin kungiyar ta G 20,a 2024 an yi taruka har sai 130 a matakan ministoci da kuma kasa da haka,kuma Amurkan ta rika halartar wasu daga cikin wadannan tarukan. Amurka dai ta yanke shawarar kin halartar taron na kungiyar G 20 da...
Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.” Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da kwarewar da tsofaffin sojoji suke da ita, haka nan kuwa darussan da su ka koya daga kallafaffen yakin kwanaki 12 da HKI. Janar Jahanshahi ya kuma ce; A wannan lokacin kwarewar da sojojin kasa na Iran suke da su, ta kai koli saboda wararrun masana da kuma amfani da fannoni mabanbanta na ilimomi, musamman kirkirarriyar Fasaha.” A dalilin hakan, sojojin suna cikin Shirin mayar wa...
Fira Ministan kasar Madagascar Herintsalama Rajaonarivelo ya gabatar da jadawalin ayyukan siyasa a gaban majalisar kasar, da a ciki ya kunshi yadda zaman gwamnatin rikon kwarya zai kasance da yadda zai kai ga yin manyan zabukan kasar a cikin shekara daya da rabi. Fira ministan kasar ta Madagascar ya kuma ce; A karshen watan farko na gwamantin rikon kwarya ne za a bude ttataunawa a fadin kasar, wanda kuma zai ci gaba har tsawon watanni shida. Daga nan kuma za a bude tataunawa akan madogarar shari’a da yi wa hukumar zaben kasar kwaskwarima. Bugu da kari, fira ministan ya ce, gwamantin rikon kwaryar za ta so shirya zabuka bayan watanni 14 zuwa 20 daga hawanta karagar Mulki. Dangane da matsalolin...
Kwamandan dakarun MDD dake kasar Lebanon ya bayyana cewa; Matukar ana son a aiwatar da kudurin MDD mai lamba 1701 kamar yadda yake, ya zama wajibi a kare hurumin kasar Lebanon. Kwamandan Dakarun Majalisar Dinkin Duniyar a Lebanon Manjo Janar Diodato Abagnara wanda ya gabatar da jawabi a lokacin da ake bikin cikar kasar Lebanon shekaru 88 da samun ‘yanci, ya kara da cewa; Sojojin kasar Lebanon abokan aikinsu ne wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kudancin Lebanon.” Har ila yau ya bayyana cewa, shigar sojojin kasar Lebanon a dukkanin yankunan kudancin kasar yana da daga cikin muhimman yunkuri na shimfida ikon gwamnati a fadin kasar. A gefe daya kwamandan sojan kasar Lebanon Rodoulf Haykal ya bayyana cewa,...
Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja. Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro. Gwamnan Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar. Sanarwar da kwamishinar ilimi ta jihar, Augustina Godwin, ya fitar ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari. Don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta....
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje. Ga jerin makarantu da abin ya shafa: Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha...
Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba. A baya Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN). Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15. A safiyar Juma’a ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar da ke yankin Papiri da ke Karamar Hukumar Agwara ta jihar Neja suka yi awon gaba da su. Da yake jawabi bayan ziyartar makarantar, ya bayyana cewa, “Na gana da iyayen ɗaliban kuma mun tabbatar musu cewa muna aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ganin an ceto yaran. Gwamnati ta ba da umarnin rufe...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a a wani taro na mayakan sa kai a nan birnin Tehran a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, da wannan dalilin ne gwamnatin kasar ta ke karfafa kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da suke da shi, su kara dankon zumunci da ke tsakanin kabilu da bangarorin kasar don hana makiya cimma manufofinsu a wannan yakin da ke yi da kasar. Yayi...
Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da...
A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka yana takurawa kasarsa ta amince da al-amura guda 28 da ya gabatar wanda a fadinsa zai kawo karshen yakin shekari kimani 3 wanda kasarsa take fafatawa da kasar Rasha. Labarin ya kara da cewa daga cikin al-amuran da shugaban ya gabatar a wannan shirin kawo karshen yaki a Ukraine sun hada da amincewa da zaben...
Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin motsa jiki daban daban. Labarin ya kara da cewa an gudanar da wasannin ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan. Tare da fara wasu wasannin daga ranar 3 ga watan. Kasar Saudiya wacce ta dauki bakwancin wadan nan wasannin motsa jiki ta sami nasarar tattara yan wasannin motsa jiki na kasashen musulmi a duniya a cikin kwanaki kima 20 da suka...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse. Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci. Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani. “Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne...
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro. Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya. Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Maharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic. Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba. Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba. Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba. Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan...
Hukumar DSS ta mayar d Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci. Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa A ranar Alhamis ne, Alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya ce DSS za su kai Kanu kowace cibiyar gyaran hali da ke Najeriya. Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da shi Sakkwato aranar Juma’a. Ya ce: “DSS ta ɗauke Mazi Nnamdi Kanu daga gidan yari na Abuja zuwa Sakkwato, sun nesanta shi da...
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare. Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta “An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris. Ya...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja Mai magana da yawun rundunar a jihar, Bright Edafe, ya ce ’yan sanda sun samu ƙorafi a kan faston bisa zargin lalata, fyade da cin zarafi. Ya ce a ranar 17 ga watan Nuwamba, an kama wanda ake zargi a harabar cocinsa. Edafe...
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar. Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a. ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Shugaban Sashen bayar da Agaji na Ƙaramar Hukumar, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula, amma bai bayar da cikakkun bayani ba. Sai dai a cikin wata sanarwa, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Abubakar Usman, ya ce bayan samun bayanan sirri tun da farko, gwamnati ta bayar...