2025-10-13@15:53:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2384
«Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe»:
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya...
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya...
Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta saki tare da hada wadanda aka yi garkuwa da su talatin da biyar tare da iyalansu. Sun kunshi mata goma sha shida da yara goma sha tara daga Kagara, Tegina da Agwara, bayan sun shafe makonni a hannun ‘yan sanda da ke tsare da kuma kawar da hankalinsu...
Masu ruwa da tsakin Arewa sun yaba da kwazon Tinubu, inda suka bukaci a kara karfafa gwiwar ‘yan kasa a taron Kaduna. Masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya sun yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa irin ci gaban da ta samu wajen cika alkawuran zabe, musamman a muhimman batutuwan da suka...
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi. Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji...
Ya ce har yanzu matsalar tsaro tana addabar sassan Nijeriya da dama, kuma ana yaudarar shugaban ƙasa game da hakan. Ya ce, “Idan Shugaba Tinubu yana sauraron labarai masu daɗi kawai daga waɗanda ke son faranta masa rai, to yana rayuwa ne a cikin duhu.” Abdullahi ya bayyana cewa al’umma da dama a Nijeriya har...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar...
Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su. Alhaji Aminu Zakari ya yi...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum....
Wadannan ’yan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi sun sake nuna bajintar da kasar Sin ke nunawa a fagen kere-keren mutum-mutumi masu siffar dan’adam da kuma yadda masana’antar bangarensu ke samun ci gaba cikin hanzari a kasar. A watan Agusta mai kamawa ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na mutum-mutumi masu...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa kyale HKI wanda kasashen duniya suka yi ne, ya ke bawa HKI karfin giwan ci gaba da abinda take yi a gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun...
Kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya taron bita tare da wadanda ba ’yan jam’iyyar ba, dangane da yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma ayyukan tattalin arziki da za a aiwatar a rabin shekarar bana ta biyu, domin sauraren ra’ayoyinsu. Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar ne ya shugabanci taron tare da...
Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu. Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai. Sun bayyana shi a matsayin mutum...

Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin...
Ministan Ƙasa na Ci Gaban Yankuna, Uba Maigari Ahmadu, ya yaba wa ci gaba da tattaunawa tsakanin jami’an gwamnati da shugabannin arewa yana mai cewa wannan “tattaunawa ce mai tarihi kuma cike da ƙarfi,” yana nuna cewa hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu ga Arewa ya fara samo asali kuma yana haifar da sakamako....
Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar. Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su...
Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi. Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna. Kwamandan...
Sakatariyar kungiyar kasashen yankin Caribeans ( Caricom) ta bayyana cewa; kasashen yankin suna son ganin bunkasa alakar kasuwanci da abokansu na nahiyar Afirka. Sakatariyar kuniyar ta kasashen Caribbian ta bayyana hakan ne a lokacin jawabin bude taron karawa juna sani a taron kasuwanci da zuba hannun jari a tsakanin yankin da nahiyar Afirka da aka...
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan,...
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar. ...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci...
Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da...

Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba
Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar...

Kwamitin Neman Sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba Ya Gabatar Da Takardar Bukatarsa Ga Majalisar Dattawa
Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba, Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim...
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi. Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye. Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin...
Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya,...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin...

Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana...
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA:...
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa...

Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil...
Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara. Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu. Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro...
Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar. Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma,...
Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare...
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum. A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko...
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar...
Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad...
A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin...
Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala...
A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara...

Babban Jami’in Hamas A Gaza; Makiya ‘Yan Sahayoniyya Suna Rufe Gazawar Sojojinsu Da Kisan Kare Dangi
Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A...
Fiye da mutane 21 ne suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kan wani coci a gabashin Kongo Rahotonni sun tabbatar da cewa; Sama da mutane 21 ne aka kashe a wani hari da mayakan ‘yan tawayen kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) suka kai kan wani cocin Katolika da ke gabashin Kongo, wanda...