Najeriya Ta Cimma Sabon Tsarin Hadin Gwiwa Kan Sha’anin Tsaro da Amurka
Published: 24th, November 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawa da tawagarta ta yi da jami’an Amurka ta kara karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa domin kara kare ‘yan Najeriya.
Tawagar, karkashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ta gana da manyan jami’an Majalisar Dokokin Amurka, Ofishin Bangaren Addini na Fadar White House, Ma’aikatar Harkokin Waje, Majalisar Tsaro ta Kasa da Ma’aikatar Yaki a birnin Washington DC
A yayin tattaunawar, tawagar ta musanta zargin kisan kare dangi a Najeriya, tana mai jaddada cewa hare-haren da ake samu na shafar al’umma ne daga bangarori daban-daban na kabilu da addinai.
Bayan ganawar, Gwamnatin Amurka ta tabbatar da kudirinta na karfafa huldar tsaro da Najeriya ta hanyar inganta musayar bayanan sirri, hanzarta aiwatar da bukatun kayan aikin tsaro, tare da yiwuwar bayar da karin kayan tsaro na musamman idan sun samu, domin tallafa wa yakin da ake yi da ‘yan ta’adda da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
Amurka ta kuma nuna shirinta na bada tallafin jin kai ga al’ummomin da rikici ya shafa a yankin Arewa ta tsakiya, da kuma taimakawa wajen karfafa tsarin ankararwa da wuri, tare da daukar mataki cikin gaggawa.
Kasashen biyu sun amince da fara aiki kai tsaye da wata yarjejeniyar hadin gwiwa da kafa Kwamitin Aiki na Hada-hadar Tsaro domin tabbatar da tsari guda wajen aiwatar da abin da aka cimma.
A nata bangaren, Najeriya ta sake nanata kudirinta na inganta tsarin kare fararen hula a fadin kasar.
Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawar ta bayar da dama wajen gyara kuskuren fahimta game da halin da ake ciki, ta karfafa amincewar juna, tare da inganta dabarun hadin gwiwa domin kare al’ummomi masu rauni musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.
Mambobin tawagar sun hada da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi; Shugaban Hafsoshin Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Daraktan Leken Asiri na Soji, Laftanar Janar Emmanuel Parker Undiandeye; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun; Daraktan Harkokin Ketare a Ofishin mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro NSA, Ambasada Ibrahim Babani; da Mai Baiwa NSA Shawara ta Musamman, Ms. Idayat Hassan.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Najeriya Tsaro Yarjejeniya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro.
Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta NejaMai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba.
Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar kowane bayani kafin su yaɗa shi domin kauce wa yaɗs labarun ƙarya.
Wannan bayani ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe manyan makarantun sakandare 41 da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, sakamakon sace ɗalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Haka kuma wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja sun rufe makarantunsu saboda matsalar tsaro.
Jihar Taraba ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da ke jihar.