Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool
Published: 24th, November 2025 GMT
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan.
A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila.
Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78.
Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18, yayin da ita kuwa Nottingham Forest ta matsa zuwa mataki na 16 da maki 12 a teburin gasar.
Kawo yanzu dai, cikin wasanni 12 da Liverpool ta buga a gasar Firimiya, ta samu nasara a wasanni 6 ne kaɗai, sannan an doke ta a sauran 6.
Wannan mummunar rashin nasara ta sake dagula wa mai horar da ƙungiyar, Arne Slot, al’amura, musamman ganin irin matsin lambar da yake fuskanta daga magoya bayan ƙungiyar a bana.
A yanzu, hankalin mai horarwar ya koma kan wasan Champions League da za su yi da PSV a ranar Laraba.
Samun nasara a wannan wasa na iya zama abin da zai ba shi damar sauƙin numfasawa; akasin haka kuma, na iya haifar masa da babbar matsala daga mahukuntan kulob ɗin da magoya bayan da ke ƙara nuna rashin haƙuri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arne Slot Firimiyar Ingila
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut
Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar Hizbullah Shahid Ali Tabatabai.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyoyi da kasashen da suka yi allawadai da hare-haren kamar haka. Akwain kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, PFLP, kungiyar falasdinawa masu gwagwarmaya (PMM), Ansarullah mai gwagwarmaya.
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen JMI da kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki duk sun yi allawadai da hare-haren sun kuma dorawa Amurka laifukan abinda HKI take aikatawa a yankin yammacin Asiya.
Dr Ali Larijani sakararen majalisar koli da tsaron kasar Iran ya yi tira da hare-haren na birnin Beirut ya kuma aza laifin kan shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda yake bawa HKI goyon baya 100% kan abinda take aikatawa a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno November 24, 2025 Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA) November 23, 2025 Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu November 23, 2025 ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba November 23, 2025 An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci