Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
Published: 26th, November 2025 GMT
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta.
Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara.
Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.”
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci dukkanin rundunonin ’yan sanda a faɗin ƙasar nan su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da aikata laifuka.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an tsaro za su ci gaba da matsa wa miyagu lamba.
Ya ce za su ci gaba da yin gwiwa da rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jami an Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye ‘Yan Sanda Daga Tsaron Manyan Mutane, Ya Amince Da Daukar Sabbin 30,000
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar da ayyukan ƙasa.
Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar sojin sama, da na ƙasa da na ruwa da Darakta Janar na ma’aikatar tsaro ta DSS da kuma Sufeto Janar na ƴansanda Kayode Egbetokun.
Sanarwar ta ce, daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa to ya nemi jami’an tsaron Nigeria Security and Civil Defence Corps.
Shugaban ƙasa ya ɗauki wannan mataki ne la’akari da cewa sassan Najeriya da dama, musamman a yankunan karkara ana fuskantar ƙarancin jami’ai ofisohin ƴansanda, lamarin da ke sanya wahalar sauye nauyin kare al’umma da aka ɗaura musu.
Tuni Shugaba Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin jami’an ƴan sanda 30,000, yayin da gwamnatin tarayya ta sanar da wani shirin haɗin gwiwa da jihohi don haɓaka cibiyoyin horar da ƴan sanda a duk faɗin ƙasar.
Daga BELLO WAKILI