Aminiya:
2025-11-25@22:18:56 GMT

Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba

Published: 26th, November 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina.

Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida.

’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba.

Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a minti na 3, sai Olakunle Alaka ya kara ta biyu a minti na 30.
A daidai minti na 45, kafin a je hutun rabin lokaci, Joseph Arumala ya rage tazara ga Ikorodu City.

Duk da wannan nasarar, Kano Pillars ta ci gaba da zama a matsayi na 20, inda take da maki 9 a ƙasan teburin gasar.

A wani labarin, ƙungiyar Katsina United ta samu nasarar doke Enyimba da ci 3–2 a birnin Ilorin, inda take buga wasanninta na gida bayan dakatar da ita daga yin wasa a filin gidan ta a Katsina.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kano Pillars Kano Pillars ta

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar

Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu suna iya kawo karshen yarjeniyar zaman lafiya da ta cimma da ita.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, kungiyar Hamas ta aiwatar da dukkan sharuddan tsagaita wuta wadanda aka dora mata, amma bangaren HKI ya ci gaba da keta tsagaita wutar tare da hare-haren da take kaiwa kan yankuna daban-daban na zirin Gaza, hare-haren da suka kai daruruwan Falasdinawa ga shahada ya zuwa yanzu.

Qassem ya ce tuni kungiyar ta shaidawa jami’an gwamnatin kasar Masar kan abinda HKI take yi na keta hurumin yarjeniyar tsagaita budewa juna wutan wanda bai kai watanni biyu ba.

Kasashen Masar, Turkiya da Qatar da Jordan da wasu kasashen larabawa da Musulmi suna daga cikin kasashen da suka dauki nauyin ganin an aiwatar da shirin tsagaita wutar kamar yadda ya dace. Amma tun bayan tsagaita wuta yahudawan basu daina kashe Falasdinawa ba. Banda haka sun ci gaba da takaita kayakin abincin da ke shigowa Gaza sabanin abinda aka cimma da ita.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare   November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza
  • Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar
  • Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool
  • NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki