Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF
Published: 23rd, November 2025 GMT
Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa fiye da yara miliyan 400 a faɗin duniya na rayuwa cikin yanayin talauci mai tsanani.
A cikin sabon rahoton da ya fitar, UNICEF ya ce ƙarin ɗaruruwan miliyoyin yara na fuskantar hatsarin faɗawa talauci sakamakon katse tallafi, rikice-rikice, da kuma sauyin yanayi da ke gurgunta samun lafiya da walwala.
Rahoton ya nuna cewa yara miliyan 118 ba sa samun uku daga cikin muhimman buƙatun rayuwa guda biyar da suka haɗa da ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki, ruwa da tsafta, da kuma muhallin da ya dace.
Haka kuma, yara miliyan 17 na rasa fiye da huɗu daga cikin waɗannan muhimman buƙatu na yau da kullum da suka zama wajibi a ce suna samu a rayuwarsu.
UNICEF ta bayyana cewa mafi yawan yaran da ke cikin mawuyacin hali na zaune ne a ƙasashen Kudu da Saharar Afrika da kuma Kudancin Asiya.
A ƙasar Chadi kadai, rahoton ya ce kashi 64% na yara ba sa samun aƙalla biyu daga cikin ababen da suka zama dole a rayuwar yaro.
Rahoton ya kuma nuna cewa matsalolin tsafta na ci gaba da addabar yara a duniya, inda kashi 65% na yaran ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ba su da damar yin amfani da makewayi mai inganci, sai kuma wasu kashi 26 a ƙasashe masu matsakaicin tattalin arziƙi, da kuma kashi 11 a manyan ƙasashe, lamarin dake barazana ga lafiyarsu.
UNICEF ta danganta wannan yanayi da yawan rikice-rikice, tasirin sauyin yanayi, basuka da su ka yi wa ƙasashe katutu, da kuma yawaitar jama’a, lamarin da gaba ɗaya ke ƙara dagula rayuwar yara a faɗin duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yara yara miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja
Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba.
A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba.
A baya Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar.
Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai mata huɗu da malamai maza takwas a yayin harin.
Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno
Ya ce makarantar na da ɗalibai 430 a ɓangaren firamare, da kuma ɗalibai 199 a ɓangaren sakandare.
Bishop ɗin ya ƙaryata zargin da Sakataran Gwamnatin Jihar Neja ya yi cewa gwamnati ko jami’an tsaro sun yi wa makarantar gargaɗi tun kafin harin.
Ya ce, “Mun tambayi Sakataren Ilimi ko ya samu wata takarda daga gwamnati, ya ce babu; ko an ce ya tura mana wata sanarwa, ma babu. Mun tambaye shi ko an sanar da shi a baki, ya ce a’a. To su faɗa wa duniya wa suka bai wa wannan takarda, ko ta wane hanya aka turo ta?
“Mun kuma tambayar Ƙungiyar Makarantu Masu zaman kansu ta Ƙasa, suma ba su samu wata irin sanarwa ba. Suka ce makarantar an rufe ta kuma an sake buɗe ta kwanaki kaɗan da suka gabata — wannan ma ba gaskiya ba ne. Mu masu bin doka ne,” in ji shi.