’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi
Published: 23rd, November 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai.
Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi.
An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN“‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.
Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.”
Ya bayyana ’yan sanda suna aikin sintiri lokacin da aka kai musu harin.
Wakil, ya bayyana sunayen ’yan sandan da suka rasa rayukansu; DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Amarhel Yunusa (10 PMF), Idris Ahmed (10 PMF), da Kofur Isah Muazu (AKU).
’Yan sandan da suka ji rauni sun haɗa da Isah Musa (SID) da Insifekta Yusuf Gambo (SID).
Ya ƙara da cewa, “Bayan samun rahoton, Shugaban ’yan sandan Ƙaramar Hukumar, SP Auwalu Ilu, ya jagoranci tawaga tare da ceto waɗanda suka jikkata.
“Sun kai waɗanda suka rasu Babban Asibitin Darazo, inda aka ajiye gawarwakin a ɗakin ajiyar gawa.
“Ana ƙokarin kama waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi tare da hukunta su,” in ji Wakil.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ziyarci wajen da lamarin ya faru, sannan miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.
“Aikin nan ba abu ne mai sauƙi ba. Duk da haka, bisa doka, za mu ci gaba da jajircewa ba dare ba rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda hari waɗanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace a cocin.
Shugaban al’umma kuma Olori Eta na Eruku, Cif Olusegun Olukotun, wanda mutane huɗu daga cikin danginsa suka kasance cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida.
Olukotun ya ce yana cikin coci tare da mutane biyar na danginsa lokacin da lamarin ya faru, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin yaran da yake kula da su ya tsere ta tagar cocin.
Ya tabbatar da cewa masu garkawan sun kira waya suna neman naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa na kowanne daga cikin mutane 38 da suka sace.
Olukotun ya yi kira da a ƙara tsaro a Eruku, wanda ke kan iyaka, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.