Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 162
Published: 24th, November 2025 GMT
162-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi.
////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda wasu makirce makircen Mu’awiya dan Abusufyan suka dabaibaye rundunar Imam Al-Hassan (a) da ta yi sansani da kusa da rundunar Ma’awiya Maskani. Inda Mu’awiya ya baza yan leken asiri suka shiga tsakanin sojojin Imam Al-Hassan(a) suna yada labaran karya, don tsoratar da su da kuma kashe guiwarsu.
Daga cikin karyayyakin da suka yada har da cewa aiki Imam Al-Hassan (a) yana musayar wasiku da Mu’awiya da nufin mayarmasa da shugabancin daular musulunci.
Banda haka mu’awiya ya sayi shuwagabannin kabilu da kwamandojin sojojin Imam Al-Hassan (a) da kudade masu yawa, sai suka koma bangaren sa. Daga cikin wadanda ya saya suka kuma sauya sheka har da shuwagabannin kabilar Kinda a lokacin.
Wannan yasa kwamandan rundunar Imam Al-Hassan (a) Ubaidullah dan Abbas a lokacin ya rubutawa Imam Al-Hassan wasika yana bashi labarin yadda sojojinsa suke sauya sheka suka komawa bangaren Mu’awiya dan Abusufyan.
Wannan kafin shi ma, Ubaidullah Mu’awiya ya aika masa na nasa yaudarar, inda ya rubuta masa wasika yana cewa wai Imam Al-Hassan (a) yana musayar wasiku da shi, dangane da mayar masu da shugabancin Al-ummar Musulmi. Don haka ya bukaci Ubaidullah, ya gaggauta zuwa wajensa, idan yayi haka to shi shugaba ne wanda za’a yi biyayya a gareshi, idan kuma ya jinkirta to zai zama mabiye, wato ba zai sami wani matsayi ba, idan shi Mu’awiya ya karbi shugabanci. Banda haka, dan sako ya nuna masa dinari 500 wanda zai karba nan take, idan ya amince sannan zai bashi wasu karin dubu 500 idan ya shiga Kufa.
Wannan wasikar ta rikita Ubaidullah dan Abbas ta kuma hanashi barci a faren da aka kawo masa ita. Inda kafin gari ya waye, ya kuduri anniyar yin Kha’inci, ya kuma fice daga rundunar Imam Al-Hassan (a) ya koma bangaren Mu’awiya dan Abusfyan, tare da rakiyar sojoji 8000 na rundunarsa.
A lokacinda gari yaw aye sai sojojin Imam Al-Hassan suka nemi kwamandansu Ubaidullahi dan Abbas don ya bada sallar Asubaha sai suka kasa gane shi. Daga baya suka fahinci cewa ya gudu ya koma bangaren Mu’awiya dan Abusufyan.
Wannan ya kara rikitasu, har zuwa lokacinda Kais dan Sa’adu dan Ubada ya zo ya bada sallah sannan yayi masu jawabi ya maida nutsuwa cikin rundunar sannan ya karbi shugabancin rundunar.
Daga baya ya rubutawa Imam Al-Hassan (a) yana masa bayanin abinda Ubaidullahi dan Abbas yayi. A lokacinda Imam (a) ya karanta wannan labarin ya yi bakin ciki sosai, ya kuma fahinci cewa mafi yawan wadanda suke tare da shi ba mutane ne da zai iya dogaro da su don samun nasara a kan Mu’awiya ba.
Ya fahinci cewa wadanda yake tare da su suna iya kamashi su mikawa Mu’awiya, zasu kha’inci shi,su kuma wargaza rundunarsa.
Ana cikin wannan Halin Mu’awiya ya ci gaba da yada karya da makirci wa Imam Al-Hassan da rundunarsa, inda ya aika zuwa Mada’in inda suka yada cewa ai, shima Kais dan Sa’ad dan Ubada shima ya canza tseka ya sulhunta da Mu’awiya ya kuma koma bangaren sa.
Suna cewa idan har an sami kan Ubaidullahi dan Abbas an saye shi, duk da cewa shi dangin Imam Al-Hassan ne, to waye kuma da ba za’a saye shi ba. Don haka kais ma bai fi karfin a saye shi ba.
Daga nan sai Imam Al-Hassan (a) ya fita birnin Kufa tare da mutane daban-daban, inda ya nufi Mada’in, a kan hanyarsa ya wuce da garuruwan Hamman Umar, da Muzlimu Saabaad.
Aka cikin wannan halin sai Mu’awiya ya aiko Abdullahi dan Amir zuwa wajen rundunar Imam Al-Hassan (a) da ke Mada’in, wanda ya zo ya tsaya a gabansu yana yana karya, saboda ya tsoratar da rundunar. A lokacinda ya karasa sai ya daga murya yana cewa: Ya ku mutanen Iraqi, ni bana ganin za’a yi yaki, ni na fito ne daga wajen Mu’awiya yake ya shigo Ambar a halin yanzu, tare da wata runduna na mutanen Sham, ku isar da gaisuwata ga –Aba Muhammad ( Imam Alhassan) ku fada masa cewa. Ina maka gargadi ka kula da kanka da kuma rayuwar wadan nan Jama’a wadanda suke tare da kai. ]]
Abin mamaka shi ne, a lokacinda suka ji wannan sanarwan ta Abdullah dan Amir sai tsoro ya shigeshi, saboda basa son mutuwa sannan suna jin tsaron ba zasu iya fuskantar rundunar Ma’awiya ba.
Banda haka Ma’awiya ya ci gaba da sayan shuwagabannin kabilun larabawan Iraki da kwamadojinsu, har suka bada labarin wai an kashe Kais dan Sa’adu dan Ubada, shugaban rundunar Imam Al-Hassan da ke Maskani.
A cikin wannan halin ne wasu daga cikin shuwagabannin kabilun larabawa a cikin rundunar Imam Al-Hassan (a) suka rubutawa Mu’awiya wasika, inda suke fada masa cewa a shirye suke su kashe Imam Alhassan idan ya bukaci hakan. Ko kuma a shirye suke su kama shi su mika shi gareshi idan yana son hakan.
A lokacinda Mu’awiya ya karbi wannan wasikar sai ya aikawa Imam Al-Hassan (a) don ya gani, ya kuma san cewa baida magoya baya, kuma yana cikin hatsari hatta a cikin sojojinsa.
Kuma a lokacinda Imam (a) ya karbi wasikun wadan nan shuwagabannin kabilun larabawa sai ya kara tabbatar da cewa su masu kha’inci ne, kuma ya sami yakini kan cewa ba zasu taba taimaka masa ba.
Ana cikin wannan halin sai Imam Al-Hassan ya aiki wani shugaba daga cikin kabilar Kinda tare da mayaka dubu 4 zuwa Ambar tare da Umarnin idan ya isa can kada ya yi kome sai umrninsa ya zo masa.
Wannan shugaban yana isa Ambar Mu’awiya ya aika masa wasika da kudade dinari dubu 500, a cikin wasikar ya ce masa, idan ka zo mani zan sanya ka sarautar a wani tsibiri wanda ba Manfasba., sai kawai ya karbi kudaden ya kuma sulale ya fice daga rundunarsa ya tare da mutane kimani 200 daga cikin makusantarsa da kuma sojojinsa da danginsa zuwa wajen Mu’awiya. Ya kha’inci Imam Al-Hassan (a).
A lokacinda labara ya zowa Imam Al-Hassan (a) sai ya yi bakin ciki, ya kuma haw Mimbari yana Khuduba, yana cewa:
{Ga Bakinde nan ya koma ya koma wajen Mu’awiya, ya kha’inceni ya kha’ineku, ya sha nanata maku kan cewa baku da cika al-kawali kuna bayin duniya ne, kuma a halin yanzu zai aika wani wanda zai maye gurbinsa, kuma lalle ni na sani zai kha’inceni da ku, zai kuma aikata abinda mutuminsa ya aikata ne, ba zai kiyaye hakkina da hakkinku ba.}
Sai Imam Al-Hassan (a) na nada wani daga cikin shuwagabannin kabilar Murad, tare da makama dubu 4, sannan ya fada masa cewa kaima zaka yaudareni, sai ya rantse kan cewa ba zai yi haka ba.
Imam yace masa: Zaka yi, mutumin ya rantse da Allah kan cewa ba zai kasance kamar wanda ya gada ba. Imam yace masa yaje, zamu gani. Yana isa Ambar, mu’awiya ya aika masa dinari dubu 500 ya yi masa alkawalin sarautar wani wuri a sham fiye da wanda ya bawa na farkon. Sai mutumin ya karbi kudaden ya kuma koma wajen Mu’awiya kamar yadda Imam (a) ya fada.
Wannan al-amarin ya sake girgiza rundunar Imam Al-Hassan fiye da yadda kuke tsammani, don da dama daga cikin shuwagabannin Kabilun larabwan Iraki sun yi kha’inci sun yi kha’inci har ya kaiga Imam ya rasa wa zai amince da shi daga cikinsu.
Al-amari ya kaiga sojojin Imam wadanda suka tare da shi a Mada’in sun debe kauna daga samun nasar a kan Mu’awiya, sai suka fara kwace kayakin juna, musamman bayan an yada kariyar cewa ankashe Kais dan Sa’adu dan Ubada a Maskani.
Banda haka sun kwace hatta dukiya Imam Al-Hassan, (a), suka kwace shimfidan da yake zama a kansa, wani ya zo ya kwace rida’insa da ke wuyansa.
Al-amarin gaba daya ya fice daga hannun Imam Al-Hassan (a). A lokacinda Mu’awiya ya tabbatar da cewa ya sami nasara a kan Imam Al-Hassan (a) sai ya aiki Mughira dan Shuba, da Abdullahi dan Amir da kuma Abdurrahman dan Hakam zuwa wajen Imam Al-Hassan (a) don su yi tattauna da shi kan sulhuntawa da kuma mika masa mulki, suna fita daga wajensa sai wasu sojojinsa suka shiga wajensa suka yi wawason kayakinsa.
Wasu malaman tarihi suna ganin, ba wadanda zasu iya aikata haka sai Khawarijawa, don sune basa ganin iyalan gidan manzon Allah (s) da wata daraja a cikin musulmi a lokacin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasa Ya Sami Halattar Makokin Shahadar Zahra (a) A Husainiyar Imam Khomani(q) November 24, 2025 Iran Da Omman Sun Tattauna Kan Al-Amuran Yankin Da Kuma Dangantaka Tsakaninsu November 24, 2025 Iran Ta Bukaci Daukar Matakan Da Suka Dace Kan Ta’asan Da HKI Ta Aikata A Beirut November 24, 2025 Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut November 24, 2025 Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno November 24, 2025 Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA) November 23, 2025 Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu November 23, 2025 ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: rundunar Imam Al Hassan A cikin wannan halin da Mu awiya ya wajen Mu awiya koma bangaren Mu awiya dan Mu awiya Ya kan cewa ba mu awiya ya Mu awiya da
এছাড়াও পড়ুন:
Zaman Majalisar Amurka Kan Zargin Kisan Kiristoci A Najeriya
Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan batun na Nijeriya.
Zaman, wanda aka yi a Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington a ranar Alhamis ya ƙunshi ’yan majalisa da masu kare hakkin dan’adam da kuma wasu kungiyoyin fararen hula.
An shafe lokaci ana lugudan laɓɓa da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran waɗanda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet.
Masu magana a wajen sun haɗa da Babban Jami’i na Cibiyar Harkokin Amurka Jonathan Pratt da Mataimakin Sakataren Cibiyar Dimokuradiyya, Hakkokin Dan’adam da Ƙwadago, Jacob McGee.
Sai kuma Daraktar Cibiyar ‘Yancin Addini, Ms Nina Shea; da Bishop Wilfred Anagbe na Cocin Katolika ta Makurdin Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Karatun Ilimin Ƙasa da Ƙasa, waɗanda suka sha tambayoyi daga ‘yan majalisar.
Yayin da wasu mambobin suka goyi bayan ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini” da daukar mataki kan Nijeriya lokacin da suke jawabi, akwai wasu daga cikin mambobin majalisar da suka bukaci a sake duba matsayin da Amurkan ta ɗauka, inda suka ce abubuwan da ke faruwa suna da sarƙaƙiya kuma suna bukatar a duba su da idon basira.
Ko da yake Shugaban Kwamitin, Chris Smith wanda ɗan jam’iyya mai mulki ta Republican ne kuma yana wakiltar Jihar New Jersey, yayin da yake jawabin bude taron ya bayyana cewa zaman yana da muhimmancin gaske, don Amurka ba za ta zuba ido kan abubuwan da suke faruwa a Nijeriya ba, kuma hakan ne ya sa yake yawan kira kan cewa akwai bukatar a dauki mataki kan ƙasar.
Sai dai wasu ’yan majalisar dokokin Amurka ba su goyi bayan matsayin Shugaba Trump kan cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya ba.
’Yar majalisar wakilai ’yar jam’iyyar adawa ta Democrat Pramila Jayapal ta ce ba ta goyon bayan daukar matakin soji a kan Nijeriya, inda ta bayyana cewa Nijeriya tana da matukar muhimmanci ga Amurka da ƙasashen Afirka.
Ta ce kashe-kashen da ke faruwa a Nijeriya ba Kiristoci kawai yake shafa ba, inda ta ce ana kashe hatta mabiya sauran addinai a kasar.