Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
Published: 27th, November 2025 GMT
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu.
Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin.
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaYa ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi.
“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi.
“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.
Sayyadi, ya ce zuwa yanzu ba su yanke inda za a yi jana’izar malamin ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.
’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSSWannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.
A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.
Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.
A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.
Cikakken rahoto na tafe…