Aminiya:
2025-11-23@21:53:59 GMT

’Yan bindiga sun kashe ɗan kasuwa, sun sace matarsa a Bauchi

Published: 24th, November 2025 GMT

Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad.

Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu

Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare.

Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici.

Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi.

Ɗan kasuwar mutum ne da ke taimakon jama’a musamman a sha’anin tsaro da kuma sabgogin maharba.

Haka kuma, ya kasance jami’in ladabtarwa a ƙungiyar First Aid ta JIBWIS a Zalau.

Zalawa, ya ce Bakoshi yana da mata biyu.

’Yan bindigar sun tafi da babbar matarsa, yayin da suka bar ƙaramar matarsa wacce ba ta jima da haihuwa ba.

Ƙoƙarin jin karin bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗan Kasuwa hari

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai da Malamai a Jihar Neja

Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu.

Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara tattara bayanai domin gano yawan mutanen da aka sace.

Wata majiya daga cocin Katolika a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ta ce har yanzu ana tattara bayanai kuma za a fitar da sanarwa nan gaba.

Kawo yanzu Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai, kuma daga bisani zasu fitar da cikakken bayani.

Shugaban sashen bada agajin gaggawa na ƙaramar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da cewa ƴan ta’addan sun kutsa makarantar ne tsakanin ƙarfe 2:00 na dare zuwa 3:00 na dare, kuma a yanzu haka ana ci gaba da tantance adadin ɗalibai da ma’aikatan da aka yi garkuwa da su.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi
  • Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu
  • An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu
  • Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu
  • DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato
  • ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai da Malamai a Jihar Neja
  • Tinubu Ya Umaurci Matawalle Ya Koma Kebbi a Cigaba da Kokarin Kubutar da Daliban da Aka Sace