Aminiya:
2025-11-27@09:12:16 GMT

’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa

Published: 27th, November 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya.

Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar.

Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau

Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere.

Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar.

Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm.

DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar Funtuwa domin dakatar da motar amma ba a ga motar ba.

Ana zargin direban da fasinjojin motar sun lura da jami’an tsaron da ke kan hanyar, wanda hakan ya sa suka zubar da jakar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yi kira ga jama’a da ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai.

Ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da sintiri da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Ya kuma gargaɗi masu aikata laifi da su guji duk wani yunƙurin tayar da zaune-tsaye, inda ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Harsasai Zariya Funtuwa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro.

Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje.

An ruwaito sun taɓa kashe ɗan sanda a shekarar 2024, kuma suna samun bayanai daga dilolin miyagun ƙwayoyi a wuraren shaƙatawa. A

An ƙwato bindiga ƙirar gida, gatari da adduna 13, mota, kwamfuta huɗu, wayoyi 13 da talabijin huɗu.

Haka kuma, a Nunbu Bashayi da ke Sanga, an kama mutane bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.

Dukkanimsu sun amsa laifinsu kuma ana neman ragowar waɗanda suke tsere.

A wani samame daban, ’yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata fashi, fyaɗe da damfara.

Sun saba kai hari gidajen mutane, ɗaukar kuɗaɗen mutane, aikata fyaɗe sannan su riƙa ɗaukar bidiyo tsoratar da mutane.

A Zariya kuwa, an kama wasu mutane tara da suka haɗa da maza da mata waɗanda ake zargi da yi wa direban Adaidaita sahu fashi ta hanyar zuba masa magani a abin sha.

Rundunar ta kuma kama wani likitan bogi mai suna Adamu Abubakar Muhammed wanda ya yi wa mutane tiyata ba tare da shaidar karatun likitanci ba.

Ya yi amfani da takardun bogi wajen yin aiki na tsawon wata guda kafin a gano shi.

Kwamishinan, ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun rundunar, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.

Ya gode wa jami’an tsaro da al’umma kan haɗin kai, inda ya yi da a ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa
  • Tsaron makarantu: ’Yan Sanda da Shugabannin Makarantu sun tsara sabbin matakai a Gombe
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi