Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK
Published: 11th, August 2025 GMT
Kakakin ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Birtaniya, ya soki kalaman da kasashen kungiyar G7 suka yi, dangane da ganin baiken ‘yan sandan yankin HK, bayan da a ranar 25 ga watan Yuli da ya shude, ‘yan sandan suka fitar da takardar sammacen cafke wasu mutane 19, masu yunkurin haifar da tashin-tashina a kasar Sin da suka tsere zuwa kasashen ketare.
A ranar Asabar ne ofishin jakadancin na kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kalamai marasa ma’ana da kasashe membobin kungiyar G7, ciki har da Birtaniya suka furta kan batun, yana mai cewa, wasu kasashe tsiraru ciki har da Birtaniya, sun tsoma baki a batun dokar tabbatar da tsaro, wadda ‘yan sandan yankin musamman na HK ke aiwatarwa, wanda hakan katsalandan ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da ma dokokin yankin na HK. Don haka, kakakin ofishin ya ce, “Muna matukar bayyana adawa da hakan.”
Jami’in ya kara da cewa, “Muna matukar goyon bayan gwamnatin yankin musamman na HK, game da yadda take aiwatar da harkokin gwamnati bisa doka, kana muna goyon bayan ‘yan sandan yankin na HK, bisa rawar da suke takawa ta kare doka, bisa la’akari da tabbatattun dokoki.”
Ya ce, yadda hadakar wadannan kasashe suka tsoma baki cikin harkokin yankin HK, ya kara fayyace matsayarsu ta yin baki biyu, da munafurci a batutuwa masu nasaba da kare hakkin bil’adama da wanzar da doka. Kuma a cewar jami’in, ba abun da hakan zai haifar sai karfafa gwiwar gwamnatin HK, wajen jagorantar yankin bisa doka da hukunta masu laifi. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a Birtaniya
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Inganta Fannin Lafiya Da Sauran Ababen More Rayuwa A Sule Tankarkar
Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma.
Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun yan siyasa na yankin da suka rasu.
Yayi bayanin cewar, za’a gina makarantun tsangayar ne a garuruwan Danzomo da Shabaru da kuma Rukutu wadanda za’a sanyawa sunan wadanda suka rasu da suka hada da marigayi Sanata Dalha Ahmad Dan Zomo da marigayi Musa Waziri Kamus da kuma marigayi Ali Ado.
Haka kuma majalisar ta amince da gyaran masallatan Juma’a na Hannun Giwa da Dan Ladin Gumel da masallacin Tsangaya na Sule Tankarkar.
Alhaji Tasi’u yace za’a gina sabbin masallatan kamsisalawati guda 5 a garuruwan Chiromawa da Kofar Yamma da kuma Babban Sara.
Majalissar ta kuma amince da gina asibitoci matsakaita guda 3 a Dan Makama da Mabia da kuma Sarkin Gandu.
Shugaban karamar hukumar yace za’a gina magudanan ruwa da kuma samar da ruwan sha mai amfani da hasken rana a garin Lula.
Har il! yau Majalisar zartarwar ta kuma amince da sayo kayayyakin gyaran tuka tuka na naira miliyan 11 da kuma amincewa da naira miliyan 5 da dubu dari 5 domin sayen magunguna da feshin maganin sauro.
Kazalika, an amince da gyaran ofishin shugaban majalissar kansiloli da kuma ofisoshin masu bada shawara guda 7 don inganta ayyukan gwamnati a yankin.
Tasi’u, yace ayyukan na daga cikin kudirorin sa guda 5 da yayi koyi da ga cikin kudirorin Gwamna 12 domin kyautata rayuwar jama’ar yankin.
Usman Mohammed Zaria