Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
Published: 26th, November 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba.
Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan.
Ya ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa iyayen yara da al’ummar Kebbi cewa ’ya’yansu sun dawo lafiya.
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro, musamman sojoji, ’yan sanda, da Civil Defence da suka yi aiki tukuru har aka kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya,” in ji Gwamnan.
Idris ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi ba ta biya kuɗin fansa ba, “Mu, a matsayin gwamnati, ba mu ba da ko sisi ba. A binciken da muka yi, babu wanda ya biya kuɗin fansar yaran.”
A ranar Litinin din da ta gabata ce ’yqn bindiga suka sace ɗaliban su 25 daga makarantar bayan sun kashe mataimakin shugaban makarantar.
Sai dai daga bisani ɗaya daga cikin ɗaliban ta gudo ’yan kwanaki bayan sace su.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kebbi Ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantu a Jihar
Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na kuɗi tare da dukkan manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Ilimi na Gaba da Sakandare Alhaji Issa Abubakar-Tunga da Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Dakta Halima Bande, a Birnin Kebbi.
Kwamishinonin sun bayyana cewa rufe makarantun gwamnati da na kuɗi a jiha ya zama dole sakamakon hare-haren da aka kai a wasu sassan jihar kwanan nan.
Sun lissafa makarantun gaba da sakandare da abin ya shafa kamar haka:
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero da Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jega da Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu da Makarantar Sharar Fagen Shiga Jami’a ta Yauri.
Sai dai sun ce makarantar da kawai ba ta cikin jerin waɗanda aka rufe ita ce Kwalejin Kiwon Lafiya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Yayin da suke kira ga dukkan shugabannin makarantun da su bi umarnin gwamnati, kwamishinonin sun shawarce su da su kasance cikin natsuwa domin za a sanar da sabuwar ranar koma makarantun nan gaba.
Sani Haruna Dutsinma