Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA)
Published: 23rd, November 2025 GMT
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi Allah wadai da kudurin da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta amince da shi kwanan nan game da shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran.
Esmail Baghai ya yi wadannan kalamai ne a matsayin martani ga kudurin da Hukumar Gwamnonin IAEA ta amince da shi, wanda Faransa, Burtaniya, Jamus, da Amurka suka gabatar.
Ya bayyana cewa kudurin ya kara dagula batun nukiliyar Iran, maimakon taimakawa wajen warware shi.
Ya kara da cewa, “A ganina, abubuwan da ke cikin wannan kuduri ba su da wani tasiri ga wadanda suka tsara shi,” in ji shi.
Ya jaddada cewa kudurin, “ba wai kawai ya karya dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ayyukan IAEA na baya ba, har ma ya kasa yin wani nuni ga tushen matsalar, wato laifukan da gwamnatin Isra’ila da Amurka suka aikata a lokacin hare-haren da suka kai wa cibiyoyin nukiliya na Iran na lumana.”
Baghai ya bayyana cewa kudurin na IAEA ya fiddo a fili tsoma baki a cikin aikin IAEA kuma zai kara kawo cikas ga ‘yancin kai na hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.
Kudurin IAEA ya bukaci Tehran ta bayar da rahoto “ba tare da bata lokaci ba” game da tarin tacaccen sinadarin uranium dinta da kuma kayayyakin da aka lalata a lokacin harin Isra’ila da Amurka a watan Yuni.
A matsayin maida martani Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a watan Satumban da ya gabata don ci gaba da hadin gwiwa da IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut November 23, 2025 Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44 November 23, 2025 Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu November 23, 2025 ‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba November 23, 2025 An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil November 23, 2025 Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci November 23, 2025 An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba November 23, 2025 An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia November 23, 2025 Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon November 23, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161 November 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana
Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.”
Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da kwarewar da tsofaffin sojoji suke da ita, haka nan kuwa darussan da su ka koya daga kallafaffen yakin kwanaki 12 da HKI.
Janar Jahanshahi ya kuma ce; A wannan lokacin kwarewar da sojojin kasa na Iran suke da su, ta kai koli saboda wararrun masana da kuma amfani da fannoni mabanbanta na ilimomi, musamman kirkirarriyar Fasaha.”
A dalilin hakan, sojojin suna cikin Shirin mayar wa da abokan gaba martani idan su ka kawo wani hari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka November 22, 2025 Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar November 22, 2025 Yan Wasan Kasar Iran Sun tashi Da Lambobin Yabo 81 A Wasannin Zumunci Tsakanin Kasashen Musulmi November 22, 2025 Shugaban Rasha yace Ba zai Janye Ayyukan Soji Da Yake Yi A Kasar Ukrain Ba November 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci