HausaTv:
2025-11-26@06:04:37 GMT

Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah

Published: 26th, November 2025 GMT

Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban  kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa.

Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana nuna irin girman kai da Isra’ila ke da shi ne.

Sayyed al-Houthi ya kara da cewa shahid al-Tabtabai ya yi kokari matuka wajen cimma manyan-manyan nasarori, kuma ya ba da gudummawa ga hanyar gwagwarmaya don taimakon  gaskiya da wadanda aka zalunta, ya kara da cewa tasirin rawar da ya taka a cikin gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa a cikin lamirin gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila a yankin.

Ya jaddada cewa Isra’ila ba za ta yi aiki da duk wani alkawari ko yarjejeniya ba, musamman idan aka yi la’akari da kariya, ta tsaro da goyon baya na siyasa da take samu ido rufe daga gwamnatin Amurka.

Al-Houthi ya jaddada cewa, tabbas Hizbullah za ta iya shawo  kan matsalolin da kalubalen da take fuskanta, saboda imaninsu da kuma dogaro da Allah, da kuma gogewa ta yau da kullum wajen tunkarar lamurra masu sarkakiya. Kuma dukkanin nasaroin da kungiyar ta samu a tsawon shekarun da suka gabata yana nuni da hakan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon

Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701.

“Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701 da kuma hurumin kasar  Lebanon.” Inji shi.

Dakarun Masu Sanya ido kan zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon UNIFIL  sun yi nazarin wurin kuma kuma tabbatar da cewa katangar ta ketare Layin da aka shata.

A cewar UNIFIL,  sun gano cewa katangar tana cikin kasar Lebanon kuma ta  kai  kimanin mita murabba’i 4,000 a cikin kasar Lebanon”.  Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa, tawagar ta sanar da sojojin na Isra’ila a hukumance  game da keta dokar da suka yi, inda suka mayar da martanin cewa za su dubi lamarin.

UNIFIL ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin, da kuma ci gaba da Magana tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da cewa an kiyaye doka da kuma yin aiki da kudiri mai lamba 1701.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
  • Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe.
  • Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Wani Kwamanda Na Mayakan Hizbullah
  •  Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Kwamandan Jihadi Haisam al-Tabtabai
  • Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44