Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki
Published: 27th, November 2025 GMT
Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.”
Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi.
Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen makamai masu linzami ya kai kolin da makiya suka kwana da sanin cewa duk wata barazana ta kawo wa jamhuriyar musulunci hari, zai fuskanci martani mai tsanani.
Haka nan kuma ya ce; Al’ummar Iran ba ta taba zama mai tsokana da fara kai hari ba a cikin kowane fada, amma kuma ba ta ja da baya a gaban barazanar makiya.
Janar din sojan na Iran ya yi Ishara da martanin da Iran din ta mayar bayan shahadar Janar Shahid Kassim Sulaimani da ya tabbatar da karfinta na kare kai. Wannan karfin ne yake hana abokan gaba tarbar aradu da ka, su kawo wa Iran din hari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare.
Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin.
A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniyar hadin kai domin kyautata rayuwar al’ummar kasar ta Yemen da kuma shimfida zaman lafiya.
A wani labari mai alaka da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta amabci cewa za a yi ganawa a tsakanin minista Abbas Arakci da takwaransa na Faransa Jean Noel Baro a gobe Laraba 26/ Nuwamba a birnin Paris.
Jigon tattaunawar shi ne bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma batun furusunonin Faransa da suke a Iran.
Haka nan kuma tattaunawar bangarorin biyu za ta tabo halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, sai kuma Shirin Iran na makamashin Nukiliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci