Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji.

Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar ma’aikatan agaji.

Bugu da kari kungiyar ta ce mutumin da aka kashe  a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba ma’aikaci ne a ma’aikatar kiwon lafiya ta Sudan.

Asibitin Zalnagi yana a jihar Darfur ta tsakiya ne da a halin yanzu ke karkashin ikon  rundunar “RSF.

A nata gefen, jami’a mai kula da tafiyar da ayyukan kungiyar ta “ Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba.”  Maryam Li Arusi ta ce, babu yadda za a yi ma’aikatansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu na jin kai a halin da ake ciki, har sai idan RSF ta bayar da tabbaci da lamunin bayar da kariya ga ma’aikatan da kuma marasa lafiya.

A daya gefen,rundunar RSF ta kore cewa tana cutar da fararen hula, tana mai jaddada cewa duk wanda aka same shi da aikata laifi to za a hukunta shi.

Tun bayan da yankin Darfur ya shiga karkashin ikon rundunar RSF ne ake fito da bayanai akan yadda mayakanta su ka aikata laifukan yaki da cin zarafin mutanen yankin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool

Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan.

A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila.

Mayaƙan Boko Haram sun file kan mata 2 a Borno Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere

Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78.

Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18, yayin da ita kuwa Nottingham Forest ta matsa zuwa mataki na 16 da maki 12 a teburin gasar.

Kawo yanzu dai, cikin wasanni 12 da Liverpool ta buga a gasar Firimiya, ta samu nasara a wasanni 6 ne kaɗai, sannan an doke ta a sauran 6.

Wannan mummunar rashin nasara ta sake dagula wa mai horar da ƙungiyar, Arne Slot, al’amura, musamman ganin irin matsin lambar da yake fuskanta daga magoya bayan ƙungiyar a bana.

A yanzu, hankalin mai horarwar ya koma kan wasan Champions League da za su yi da PSV a ranar Laraba.

Samun nasara a wannan wasa na iya zama abin da zai ba shi damar sauƙin numfasawa; akasin haka kuma, na iya haifar masa da babbar matsala daga mahukuntan kulob ɗin da magoya bayan da ke ƙara nuna rashin haƙuri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare  
  • Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen
  • Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool
  • Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji
  • Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta
  • Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno
  • Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44
  • Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci