ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
Published: 27th, November 2025 GMT
Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”
Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.”
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugabannin sun ce gabanin sanarwar, kasar na cikin shirin sauraron sakamakon zaben da aka yi, wanda suka ce ya gudana lami lafiya.
A halin da ake ciki dai Sojojin da suka kwace mulki a Guinea-Bissau sun rantsar da Horta N’Tam a matsayin sabon shugaban riko na tsawon shekara daya.
Janar N’Tam ya sha rantsuwa ne yau alhamis a hedikwatar sojojin da ke babban birnin kasar Bissau, bayan da suka hambarar da shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo a jiya Laraba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bin diddigin lamarin da “matukar damuwa,” tana kira da a girmama bin doka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana
Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su.
Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu.
Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare da sace mutane da kashe su da kuma kama su a tafi da su inda ba wanda ya sani. Wannan ya sa a dole mutanen yankin suka fito suna neman sauyi da kuma kawo karshen wannan musibar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci